Dole wanda zai yi takarar Gwamnan Jigawa ya san harkar gona – Badaru

Dole wanda zai yi takarar Gwamnan Jigawa ya san harkar gona – Badaru

Mai girma gwanmna Muhammadu Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ya ce ya zama dole ga ‘dan takarar gwamna a 2023 ya kware a harkar noma.

Muhammadu Badaru Abubakar ya ce duk wanda zai rikewa jam’iyyar APC mai mulki tuta a zaben 2023 a jihar Jigawa, sai ya zama ya na da ilmin aikin gona.

Jaridar Tribune ta rahoto gwamnan ya na wannan jawabi ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2020.

A karshen makon nan Badaru Abubakar ya jagoranci shuka itatuwa a garin Garki da ke jihar Jigawa, inda a nan ya yi magana game da wanda zai gaje shi.

A cewarsa, yadda jihar Jigawa ta dogara da noma, ya kamata duk wanda zai yi mulki a jihar ya zama ya lakanci aikin noma domin kawowa al’umma cigaba.

Gwamnan bai bayyana sunan wani dan siyasa da ya ke ganin ya fi dacewa da zama gwamna a 2023 ba, sai dai kawai ya ba sanin harkar noma muhimmanci.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya soma bada damar bude kasuwanni

Dole wanda zai yi takarar Gwamnan Jigawa ya san harkar gona – Badaru
Badaru Abubakar na Jigawa
Asali: UGC

Da ya ke jawabi, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce Jigawa ta na da filin noman da mutane za su iya yin shuka har sau uku a cikin shekara.

Mai girma gwamnan, ya ce an ga sauyi sosai a bangaren noma a mulkinsa, domin ya yi imani ta harkar noma ne za a samawa dinbin mutanen jihar Jigawa abin yi.

Hanyar da za a bi wajen bunkasa noma shi ne inganta kasa inji gwamnan. Badaru Abubakar ya ce bincike ya nuna cewa bishiyar gawo ta na da matukar amfani.

Wannan ya sa aka rika shuka bishiyar gawon domin hana zaizayewar kasa a Jigawa. Gwamnan ya yi kira ga kananan hukumomi da sauran jama’a su guji sara itatuwa sosai.

“Za mu karfafa dokokin da su ka haramta datse itatuwa a jihar nan, za mu ba manoma damar cin moriyar wadannan itatuwa masu muhimmanci.’ Inji gwamnan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel