Kotu Ta Ci Tarar Dan Takarar Gwamna a ADC Miliyoyi kan Fastocin Siyasa a Adamawa

Kotu Ta Ci Tarar Dan Takarar Gwamna a ADC Miliyoyi kan Fastocin Siyasa a Adamawa

  • Kotun Majistare da ke Yola ta ci tarar ɗan takarar gwamna a jam'iyyar ADC na 2027 kan manna fastocin siyasa
  • Kotun ta bayyana cewa shari'ar ba ta ci gaba a matsayin laifi ba, domin ba a gurfanar da wanda ake ƙara ba, ba a karanta masa tuhuma ba
  • Hukumomin Adamawa sun ce hukuncin zai zama gargaɗi ga 'yan siyasa, suna jaddada cewa yaƙin neman zaɓe dole ya mutunta dokokin muhalli da tsara birane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar ADC mai adawa ya gamu da fushin wata kotu kan lika fastocin siyasa a wasu wurare.

Kotun Majistare ta 2 da ke Yola ta ci tarar ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC na zaɓen 2027 a Adamawa, Omar Suleiman, Naira miliyan uku.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

An ci tarar dan takarar gwamnan ADC
Dan takarar gwamna a ADC, Omar Sulaiman a hagu da babbar kotun tarayya. Hoto: Omar Sulaiman.
Source: Facebook

Rahoton TVC News ya tabbayar da cewa an ci tarar dan siyasar ne saboda liƙa fastocin yaƙin neman zaɓe.

Zargin da kotun ke yi kan dan siyasar

Kotun ta ce an liƙa fastocin a kan gine-ginen gwamnati da wuraren jama'a a babban birnin Adamawa, abin da ya saɓa wa dokokin muhalli da tsara birane.

Babban Alƙali Musa Adamu ne ya yanke hukuncin bayan ƙarar da Ma'aikatar Muhalli ta Adamawa, Hukumar Tsara Birane da Babban Lauyan Adamawa suka shigar.

Kotun ta bayyana cewa duk da an fara shigar da ƙarar a matsayin ta laifi, daga baya an mayar da ita shari'ar gudanarwa saboda wanda ake ƙara bai halarci kotu ba.

Dan takarar ADC ya gamu da fushin kotu kan lika fastoci
Taswirar jihar Adamawa da APC ke mulki a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin lauyan dan siyasar ya ce a kotu

Alƙalin ya ce ba a gurfanar da Omar Suleiman ba, ba a karanta masa tuhuma ba, sannan ba a karɓi amsa daga gare shi ba kafin zaman kotun, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Da gaske alkalin da ya ba Tinubu nasara a kotu a zaben 2023 ya makance?

Lauyan Omar Suleiman, Barista Bala Sanga, ya shaida wa manema labarai cewa kotun ta yanke hukuncin tara ta gudanarwa ta Naira miliyan uku saboda liƙa fastoci ba bisa ƙa'ida ba.

An zargi fastocin ɗan takarar da bayyana a wurare kamar gadar sama ta Unity da shataletalen Jippu-Jam da Mai Doki, abin da ya saɓa wa umarnin zartarwa kan tallace-tallace.

Hukumomi sun ce hukuncin zai zama gargaɗi ga masu siyasa kafin fara yaƙin neman zaɓen shekarar 2027, tare da jaddada cewa dole a mutunta dokokin muhalli da tsara birane.

Tsagin ADC ya dakatar da Atiku, Babachir

A wani labarin, an ji cewa wani tsagi na ADC a jihar Adamawa ƙarƙashin Raji Zumo ya yi taron sanar da dakatar da Atiku Abubakar da wasu mutane biyu daga jam'iyyar.

Raji Zumo ya zargi Atiku da sauran mutanen da hannu wajen ƙirƙirar rassan bogi a jam'iyyar, raunana tsarin shugabanci, da yin watsi da umarnin kotu .

Sai dai Babachir Lawal, wanda shi ma aka dakatar da shi, ya bayyana kwamitin Raji a matsayin "masu shan wiwi" wadanda ƙwaya ta bugar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.