Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC

Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC

- Terkimbi Ikyange yana shirin sauya sheka zuwa jami'yyar APC

- Shugaban jam'iyyar APC na jihar Benue Abba Yaro ne ya sanar da cewa tsohon Kakakin Majalisar Jihar zai sauya sheka

- An ganin komawar Ikyange jam'iyyar ta APC zai ƙara wa jam'iyyar ƙarfi da karɓuwa

Terkimbi Ikyange, tsohon Kakakin Majalisar Jihar Benue yana shirye shiryen komawa jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Kwamared Abba Yaro, shugaban jam'iyyar APC na jihar Benue ne ya sanar da hakan inda ya ƙara da cewa jam'iyyar tana maraba da tsaffi da sabbin mambobi kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Yaro ya ce tsohon Kakakin Majalisar mutum ne mai matukar muhimmanci ga jam'iyyar kuma komawarsa zai ƙarfafa jam'iyyar APC a jihar ta Benue.

Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC
Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Uganda: Matashi ɗan shekara 19 ya fito takarar shugaban kasa

Kafin sanar da dawowar Iyange, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Yakubu Dogara shima ya fice daga jam'iyyar PDP ya komo APC.

An sanar da labarin komawarsa APC ne bayan Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa a ranar Juma'a 24 ga watan Yulin 2020.

A bangarensa, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce bai shirya barin jam'iyyar PDP ba don komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC.

Ortom ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya yi wurin taron PDP da aka zabi sabbin shugabannin jam'iyyar jihar don fayyace gaskiya kan iƙirarin da wasu ke yi na cewa zai koma APC.

Gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar ta APC ta masa tayi amma ba shi da niyyar komawa saboda abinda ke gabansa shine gina jam'iyyar adawar ta PDP.

Duk da hakan, Ortom ya ce yanayin jajircewar sabbin shugabanni jam'iyyar da aka rantsar ne zai tabbatar da zamansa a jam'iyyar ko akasin hakan.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, jam'iyyar APC ta yi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya hakura ya dawo jam'iyyar.

Jam'iyyar ta kuma mika irin wannan gayyatar ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da wasu tsaffin ƴan jam'iyyar ta suka fice tun 2015.

A cewar jam'iyyar mai mulki, dawowar Sanata Barnabas Gemade da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara alama ce da ke nuna sulhun da kwamitin riko na Mai Mala Buni ke yi na samun nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel