Siyasar Najeriya
Rade-radin na yawo cewa PDP ta fara shiga rikici kan wanda za ta ba tikiti a 2023. Sai dai jam’iyyar tace ba ta dauki wata matsaya game da tikitin takarar shugaban kasa na 2023 ba tukun.
Akwai bakaken Aljanu a gidan gwamnan jihar Anambra kamar yadda Gwamna ya fada har ya nemi jama’a su yi masa addu’a kan wasu Aljanu da ke damunsa har ya gaza aiki.
Kotun daukaka kara dake zamanta a garin Jos ta sutale wani dan majalisa daga jam’iyyar APC, Alhaji Garba Muhammad Gololo daga kujerar da yayi dare dare a kai bayan ta kamashi da laifin amfani da takardun karatu na bogi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar Kebbi, KESIEC ta sanar da jam’iyyar APC mai mulki a jahar ta lashe dukkanin kujerun da aka fafata a zaben kananan hukumomin jahar na ranar 26 ga watan Oktoba.
Sanatan nan na PDP, Suleiman Asonya Adokwe ya yi bankwana da siyasa bayan ya rasa kara a kotun zabe. Tsohon Gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura ne ya yi wa ‘Dan takarar PDP a zaben na 2019 ritaya.
A yayin da zaben gwamnan jihar Kogi ke kara karato wa, 'yan kabilar Igala a karkashin jagorancin sabon mataimakin gwamna jihar Kogi, Edward Unekwuojo Onojo (CIK), Sanata Jibrin Isa Echocho, da sauran zababbun mambobin jam'iyyar AP
Majalisar dokokin jahar Gombe ta umarci diyar tsohon gwamnan jahar Gombe, Sanata Danjuma Goje ta ‘rusuna ta tafi’ a yayin da ta bayyana a gabansu domin yan majalisar su tantanceta don zama kwamishina.
Majalisar dokokin jahar Gombe za ta tantance diyar tsohon gwamnan jahar, Sanata Danjuma Goje wanda gwamnan jahar Muhammadu Inuwa Yahaya ya aika musu da nufin nadata mukamin kwamishina.
Kungiya AIED ta yi tir da shirin cafke Fisayo Soyombo a dalilin bankado irin rashin gaskiyar da ‘yan sanda da gandurobobin kasar su ke yi a Najeriya.
Siyasar Najeriya
Samu kari