Abin da Ya Faru tsakani Na da Ta In ji Malamin da Ake Zargi da Neman Matar Aure
- Dr. Nasa'i Muhammad Gwadabe ya fadi bangarensa a zargin da ake yi masa na neman yin lalata da dalibarsa mai aure
- Malamin jami’ar ya ce babu inda ya nemi Sa’adatu Kabir Uba, sai dai ta shirya masa tarko ne saboda wata manufa
- Gwadabe ya bada labarin yadda ya hadu da dalibar har zuwa ranar da aka yi masa duka da sunan an kama mazinaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al'ada
Jihar Kano - Kwanan nan labari ya karade ko ina ana zargin wani malami da neman dalibarsa a jami’ar Maryam Abacha a jihar Kano.
An ce wannan mata tana da aure amma malamin yake bibiyar ta kuma ya yi shekaru biyu ya hana ta kammala binciken da ta ke yi.

Source: Facebook
Nasa'i Muhammad Gwadabe ya wanke kan shi
A Facebook, tashar Lumana ta yi magana da shi domin jin ta bakinsa, kuma ya yi bayanin abin da ya ce shi ne hakikanin abin da ya wakana.

Kara karanta wannan
"Fatan za ku yi kewata"; Wasiyyar da Trump ya bari idan Iran ta samu nasarar kashe shi
Malamin jami’ar ya ce sunan wannan daliba Sa’adatu Kabir Uba kuma bai son abin da ya sa ta shirya masa zargin neman ta haka kurum.
Dr. Nasa'i Muhammad Gwadabe malami ne a sashen siyasa da ilmin alakar kasashe a jami’ar Northwest amma ya je aiki a MAUN.
Bayan nan kuma Nasa'i Gwadabe ya tafi aikin hutu a jami’ar Baba Ahmad ko da Freedom Radio ta rahoto MAUN ta nesanta kan ta da sho.
Jami'ar MAUN ta hada Gwadabe da Sa'adatu
Ya ce da jami’ar Maryam Abacha ta tashi rabon daliban da za su yi binciken samun shaidar digiri, sai aka tura masa Sa’adatu Uba.
Amma jami’ar ba ta ba shi ajin da zai koyar da masu digirin farko ba, aka ce za su dauki masu digirgir ne don haka bai shiga jami’ar sosai.
Saboda haka ne ma ya ce ya nemi a raba shi da dalibar, a hada ta da sauran kananan malamai da suke karantar da masu neman digirin farko.
A haka ya cigaba da duba aikin dalibar da wasu takwas tunda an biya shi albashi a Mayun 2026 amma da nufin su hadu a jami’ar Baba Ahmad.
Dr. Gwadabe ya ce a wata litinin suka hadu da Sa’adatu Uba a cikin wani aji a jami’ar ta Sharada, ya yi mata gyare-gyaren aikin da ta ke yi.
Ya ce a ranar Laraba ta kira shi tana cewa ba ta fahimci gyare-gyaren da a yi ba, ta ce ‘akwai bukatar mu zauna.’
Shi kuma sai ya ce ba zai fita a ranar ba kuma yana da aji da zai koyar ranar Alhamis, Juma’a kuma bai shiga jami’a amma ya taimaka mata.
Ganin yadda ta matsa masa, sai ya ce yakan je sakatariyar ASUU da maraice, amma don haka ta nemi su zauna ranar Asabar ya duba aikin nata.
Malamin ya zargi dalibar da yanke hirarrakin da suka yi, ya ce ita da kan ta ta kawo shawarar su hadu a wajen cin abinci da ya nemi inda za a gana.
'Tarkon' da dalibar ta shirya wa malamin jami'ar
Ya ce a lokacin da ta zo makarantar, sai ta rika yi kamar ba ta gane sakatariyar ASUU ba, har ta jawo shi ya zo wani wuri da nufin ya gan ta.
Da suka hadu ta ajiye mota a tsakiyar titi kuma ya ce ya shiga gaban motarta a karshe domin yin abin da ya kawo su, ana haka sai aka shake shi.
Nasa'i Muhammad Gwadabe ya ce:
“Ina zama ko gaisuwa ba mu yi ba, sai na ji an shako ni. Ashe akwai wani mutum a baya.

Source: Instagram
Daga nan ne kuma ya ce aka rufe motar aka wuce da shi, kuma aka fada wa dalibar ta je ta kira ragowar mutanen da aka tanada, suka yi masa duka.
Gwadabe ya ce haka aka lakada masa duka kuma aka rika fada wa jama’a cewa an kama shi ne yana zina da matar aure har da masu neman kashe shi.
“Suna dukan, akwai wanda ya zaro wuka ya ce zai kashe ni. Da aka ga ya zaro wuka ne sai mutane suka rike shi, kuma ya ce ko ba yau ba sai ya kashe ni.
- Nasa'i Muhammad Gwadabe
Da jami’an tsaro suka cece shi sai aka kai shi asibiti domin yana zubar da jini. Bayan an gama kula da shi ya ce aka nemi duka mutanen aka rasa.
Malamin jami'ar ya karyata zargin neman matar aure
A hirar da aka yi, ya tabbatar da cewa a Nuwamban 2025 suka fara aiki, ya karyata zargin da ake yi na shafe shekaru har biyu ya hana ta gama aiki.
Malamin ya rantse da Allah SWT cewa babu abu mai kama da lalata da ya faru tsakaninsu, ya ce idan an yi, ka da Ubangiji ya ba shi abin da yake nema.
A cewarsa, watakila ta yi wannan ne saboda ta wanke kanta a wajen mijinta idan har yana zarginta da laifin cin amanar aure ko don ta gama makaranta.
“Watakila tana son tabbatar masa da cewa ita kamammiya ce, sai ta yi amfani da ni, ta ci zali na”
- Nasa'i Muhammad Gwadabe
Jami'ar MAUN ta rufe wurin kwanan dalibai
Kwanaki an ji labarin hukumar gudanarwar jami'ar ta ba da umarnin gaggawa na rufe wasu dakunan kwanan dalibai mata guda biyu mallakin masu zaman kansu.
An rufe Al-Ansar da Indabo da ke kan titin Hotoro da UDB a birnin Kano. An dauki wannan matakin ne saboda zargin rashin da'a, lalata, raba dakunan ga baki.
Mahukanta sun gano ana fama da fitar dare ba tare da izini ba, da kuma matsalolin karancin ruwa da wutar lantarki da ke barazana ga tsaron daliban jami'ar.
Asali: Legit.ng



