Gwamna Abba Ya Garzaya Wurin Kashim Shettima bayan Tinubu Ya Zaɓi Abokin Takara a 2027

Gwamna Abba Ya Garzaya Wurin Kashim Shettima bayan Tinubu Ya Zaɓi Abokin Takara a 2027

  • Gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya taya Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, murnar sake zama abokin takarar Bola Tinubu
  • Ya ce nadin ya nuna irin gudunmawar da Shettima ke bayarwa ga ci gaban Najeriya guj daga hawa kan mulki zuwa yau
  • Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya ba Tinubu da Shettima lafiya da nasara a zaben 2027, tare da sake jaddada goyon bayansa ga hadin kan kasa da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, murnar sake zama abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Abba ya tura sakon taya murna da fatan alheri ga Shettima bayan APC ta ayyana shi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi dabara, an gano hikimar ci gaba da tafiya da Kashim Shettima

Abba.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa Gwamnan ya kai ziyarar gaisuwa ga Shettima a daren Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2026 a Aguda House da ke Fadar Shugaban Kasa a Abuja.

Gwamnan na Kano ya sake jaddada goyon bayansa da kuma yi wa Sanata Shettima fatan alheri yayin da shirye-shiryen babban zaben 2027 ke ƙara kankama.

Abba Gida-Gida ya yabawa Shettima

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Darakta Janar na Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A sanarwar, Gwamna Sbba Kabir Yusuf ya bayyana cewa sake zaben Shettima a matsayin mataimakin dan takara wata shaida ce ta irin jajircewa, sadaukarwa da hidimar da yake yi wa kasa.

Ya ce hakan ya nuna yadda aka amince da kwarewar Kashim Shettima da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban Najeriya baki daya.

Ya yi addu'a ga Tinubu da Shettima

Kara karanta wannan

Kwankwason APC ya ari bakin 'yan Arewa, ya yi magana kan tikitin Tinubu da Shettima a 2027

Gwamna Sbba ya kuma yi addu'ar Allah Ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, hikima, lafiya da nasara yayin da suke shirin tunkarar babban zaben shekarar 2027.

A yayin ziyarar, Gwamna Yusuf ya sake bayyana goyon bayansa ga duk wani shiri da zai inganta hadin kan kasa, zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Mutanen da suka raka gwamnan sun hada da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gwale, Hon. Injiniya Garba Diso d mamban kwamitin gudanarwa na APC ta kasa, Hon. Muhammad Jamu Yusuf.

Haka zalika Kwamishinan Harkokin Addini na jihar Kano, Sheikh Ahmad Tijjani Auwalu na cikin tawagar Gwamma Abba da ta ziyarci Kashim Shettima a Abuja.

Kwankwaso ya jinjinawa Tinubu

Kun ji cewa jigon APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yabawa Shugaha Bola Tinubu kan sake daukar Kashim Shettima a matsayinNmataimaki.

A cewarsa, matakin da Shugaba Tinubu ya dauka ya kara wa jam'iyyar APC karfi a yankin Arewa tare da kara wa al'umma kwarin gwiwa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Ya ce zaben Shettima ya bai wa APC cikakken karfi a yankin Arewa, yana mai cewa yankin a shirye yake ya sake marawa tikitin Tinubu daNShettima baya domin samun wa'adi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262