‘Yan Bindiga Sun Sace Gawar Babban Jami’in FRSC da Masu Rakiyarta a Hanyar Jana’iza

‘Yan Bindiga Sun Sace Gawar Babban Jami’in FRSC da Masu Rakiyarta a Hanyar Jana’iza

  • Ana zargin ‘yan bindiga sun tare motar da ke ɗauke da gawar tsohon babban jami’in FRSC, Augustine O. Ikwue, a jihar Kogi
  • Rahotanni sun nuna cewa gawar da mutane tara, ciki har da jami’an FRSC biyu, sun fada hannun masu garkuwa da mutane
  • Sai dai bayanai sun nuna cewa daga baya an gano gawar marigayin a garin Ejule, inda aka mika ta ga iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari kan motar da ke dauke da gawar tsohon Mataimakin Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), Augustine O. Ikwue.

Maharan sun sace gawar da kuma mutanen da ke rakiyar ta zuwa garinsu na Otukpo da ke jihar Benue.

Jihar Kogi.
Taswirar jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis da ta wuce a hanyar Ochadamu zuwa Ejule da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Ginin Majalisar dokokin jihar Gombe ya rufta kan mutane ana tsakiyar aiki

Marigayi jami'in FRSC ya rasu ne a Osogbo, babban birnin jihar Osun, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Yan bindiga sun bukaci Naira miliyan 450

Rahotanni sun ce masu garkuwar sun tuntubi iyalan marigayin tare da neman a biya kudin fansa har Naira miliyan 450 domin sakin mutanen da suke tsare da su.

Kwamandan FRSC na jihar Kogi, Lawal Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutum tara ne aka yi garkuwa da su, ciki har da jami’an FRSC biyu da ke cikin tawagar zuwa jana’izar.

Hukumar FRSC ta gano gawar Ikwue

Sai dai ya bayyana cewa daga baya an gano gawar marigayin a yankin Ejule, inda aka mika ta ga iyalansa domin gudanar da jana’izarsa.

Ya ce:

“Mun gano gawar marigayin a garin Ejule a ranar Juma’a bayan bincike mai zurfi, sannan muka mika ta ga iyalansa. An birne shi a ranar Asabar a garinsu na Otukpo da ke jihar Benue.”
Jami'an FRSC.
Jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a bakin aiki Hoto: FRSC
Source: Twitter

Fagge ya ce masu garkuwar sun yi amfani da wayar marigayin wajen kiran matarsa domin sanar da ita bukatar kudin fansa.

Kara karanta wannan

Guguwa mai ƙarfi ta kashe mutane, ta yi mummunar ɓarna a garuruwa fiye da 100 a Jigawa

“Masu garkuwar sun yi amfani da wayar marigayin suka kira matarsa, inda suka bukaci a biya makudan kudade domin sakin mutanen da suke tsare da su," in ji shi.

Matakin da jami'an tsaro suka dauka

Rahotanni sun ce jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, mafarauta da masu sintiri sun bazama yankin domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da kamo wadanda suka kai harin.

Lamarin ya janyo martani daga mutane da dama, inda suka nuna damuwa cewa har gawar mamaci ba ta tsira daga hare-haren ‘yan bindiga ba.

Yan bindiga sun sace dalibai 3

A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga sun kutsa masaukin daliban Jami'ar Tarayya ta Lafia da ke jihar Nasarawa, tre da yin awon gaba da mutum uku.

An ce 'yan ta'addar sun farmaki gidan kwanan daliban ne da ke a kan titin Awe, kusa da matsugunnin jami'ar na wucin gadi da ke Akunza a Lafia, jihar Nasarawa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya umarci tura jami'an musamman da masu sintiri domin gudanar da aikin ceto a cikin dazukan da ke kewaye da yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262