Mujallar Tell ta ba Farfesa Babagana Zulum kyautar Gwamnan shekara

Mujallar Tell ta ba Farfesa Babagana Zulum kyautar Gwamnan shekara

A ranar Litinin, 17 ga watan Agusta, 2020, mujallar Tell ta Najeriya ta ba gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, mamaki da kyautar gwamnan shekara.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya lashe kyautar wannan shekara ta 2020 ne saboda tsayawa tsayin dakar da ya nuna a watanni kimanin 15 da ya yi a kan mulki.

Shugaba kuma babban editan mujallar Tell, Mista Nosa Igiebor, ya jagoranci kamfaninsa zuwa jihar Borno da wannan kyauta da takarda domin a mikawa gwamnan.

Tell ta na cikin tsofaffin mujallun da ake da su a Najeriya, an fara buga ta ne a shekarar 1991.

Kamar yadda mu ka samu labari daga shafin gwamna Babagana Zulum, ma’aikatan mujallar sun dura babban birnin jihar Borno ne ba tare da sanin gwamnan ba.

Mujallar ta gayyaci mai girma gwamna Babagana Zulum da sauran jama’a zuwa wajen taron da ta shirya a katafaren dakin taro na gidan gwamnati da ke garin Maiduguri.

KU KARANTA: 2023: Badaru ya bayyana wanda zai tsaya takarar Gwamnan Jihar Jigawa

Mujallar Tell ta ba Farfesa Babagana Zulum kyautar Gwamnan shekara
Babagana Zulum ya ci kyautar TELL
Asali: Twitter

A wajen wannan taro ne aka ba gwamnan mamaki, aka ba shi kyautar lambar yabo. Wadanda su ka yi wa Nosa Igiebor rakiya su ne, Dejo Oyawale da Wola Adeyemo.

Manema labarai sun ce wannan ne karon farko da gidan jarida za ta bi gwamna har gida ta mika masa lambar yabo, an saba bada wannan kyaututtuka ne a manyan Birane.

Nosa Igebor ya ce Zulum ya lashe wannan kyauta ne a dalilin kokarin da ya nuna wajen kare rayukan mutanen jihar Borno tun daga ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

“Shugabanci ya kunshi jajircewa da tsayin daka wajen hidimar al’umma da sadaukar da kai domin cigaban jama’an da ake mulka.” Inji Mista Nosa Igebor.

Nosa Igebor ya kara da cewa: “Daga lokacin da ka hau kan karagar mulki a matsayin gwamna, ka nuna wadannan halaye a shugabancinka."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel