Tinubu Ya Yi Dabara, an Gano Hikimar Ci Gaba da Tafiya da Kashim Shettima
- Fadar Shugaban Kasa ta yi magana game da hikimar daukar Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa
- Ta ce ci gaba da rike Kashim Shettima a zai kare hadin kan APC, tare da dakile rikicin siyasa kafin zaben 2027
- Stanley Nkwocha ya ce Shettima ya tabbatar da kwarewa, aminci da jajircewa, da taka muhimmiyar rawa a gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta bayyana hikimar ci gaba da tafiya da Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Fadar ta ce duk da karfin tikitin Tinubu da Shettima, APC sai ta gamsar da 'yan Najeriya da sakamakon ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
Hadimi na musamman a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha shi ya bayyana haka a shafin X.
Matsalar maye gurbin Shettima a matsayin mataimaki
Sanarwar ta bayyana cewa maye gurbin Shettima zai iya girgiza zaman lafiyar jam'iyyar APC.
Stanley Nkwocha, ya ce Tinubu ya yanke wannan hukunci ne saboda amincewa da Shettima.
Ya ce aminci, kwarewa da yadda Shettima ya gudanar da aikinsa sun taimaka wajen dorewar gwamnatin tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023.
Nkwocha ya ce matakin ya kawo karshen rade-radin da aka dade ana yi kan makomar siyasar Shettima.
Ya kara da cewa hakan ya sake tabbatar da hadin gwiwar da ta bai wa APC nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
A cewarsa, maye gurbin Mataimakin Shugaban Kasa zai iya haddasa rashin daidaito a cikin jam'iyyar tare da bai wa 'yan adawa damar amfani da rabuwar kai wajen cimma manufofinsu.
Ya ce ci gaba da rike Shettima ya dakile damuwar siyasa da ta mamaye jam'iyyar, tare da tabbatar da cewa hadin gwiwar Tinubu da Shettima na nan daram.
Nkwocha ya bayyana cewa Shettima ya samu cikakkiyar amincewar Shugaban Kasa ne saboda biyayya, jajircewa da kuma yadda yake aiwatar da manyan ayyukan kasa cikin nasara.
Ya ce Shettima, a matsayinsa na shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC), ya jagoranci tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi kan sauye-sauyen tattalin arziki.
Haka kuma ya ce an tattauna batutuwan tsaron abinci, noma, samar da ababen more rayuwa, kirkire-kirkiren fasahar zamani, inganta abinci mai gina jiki da ci gaban jihohi.
Nkwocha ya ce Shettima ya kasance yana kare manufofin gwamnatin Tinubu tare da gudanar da aikinsa cikin iyakokin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya bayyana Mataimakin Shugaban Kasan a matsayin abin dogaro wanda ya taimaka wajen karfafa hadin kai da fahimtar juna a cikin gwamnatin Tinubu.
Ya kuma tabo batun tikitin Musulmi da Musulmi na APC a zaben 2023, yana mai cewa an zabi hakan ne bisa kwarewa, gogewar shugabanci da dabarun siyasa, ba saboda addini ba.
Kiristocin Arewa sun goyi bayan Shettima
An ji cewa wata kungiyar Kiristoci a yankin Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki.
Shugaban kungiyar, Fasto Jolly Usman, ya ce ƙwarewar Shettima da haɗin gwiwarsa da Tinubu sun taimaka wajen inganta tsaro.
Ƙungiyar ta bukaci 'yan Najeriya su yi hukunci kan shugabanni bisa ayyukansu da nagartarsu, ba wai la'akari da bambancin addini kaɗai ba.
Asali: Legit.ng

