Alaka Ta Munana: An Hada Baki da Sojoji Aka Tsare Dan Majalisar Amurka a Isra’ila

Alaka Ta Munana: An Hada Baki da Sojoji Aka Tsare Dan Majalisar Amurka a Isra’ila

  • Dan majalisar dokokin Amurka Ro Khanna ya zargi wasu Yahudawan Isra'ila da tsare shi tare da wasu Amurkawa
  • Dan siyasar ya ce sojojin Isra'ila sun goyi bayan mazauna yankin yayin da rundunar IDF ta musanta hannu a lamarin
  • Lamarin ya sake jawo hankali kan karuwar rikice-rikice a Yammacin Kogin Jordan tun bayan fara yakin Gaza a watan Oktoban 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Dan majalisar wakilan Amurka daga jihar California, Ro Khanna, ya zargi wasu Yahudawa da cin mutuncinsa.

Khanna ya ce wasu Yahudawan Isra'ila masu dauke da makamai sun tsare shi tare da wasu Amurkawa.

Sojojin Isra'ila sun tsare dan majalisar Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump (hagu) da Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu (dama). Hoto: Chip Somodevilla and Ronen Zvulun / POOL / AFP.
Source: UGC

A wani sako da ya wallafa a shafin X, Khanna ya ce mazaunan yankin dauke da bindigogin M4 da Amurka ta kera sun tare su.

Kara karanta wannan

Matashi mai shekaru 23 ya hallaka Farfesa da kaninsa cikin wani irin yanayi

Yadda Yahudawa suka tsare dan majalisar Amurka

Khanna ya bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin wata ziyara da suka kai yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ke mamaye da iko.

Sai dai Rundunar Tsaron Isra'ila (IDF) ta musanta zargin cewa dakarunta sun taka rawa wajen hana Khanna da tawagarsa ci gaba da tafiya.

Ya kara da cewa bayan sojojin Isra'ila sun isa wurin, sun goyi bayan mazaunan yankin kuma suka ci gaba da tsare su na wani lokaci.

Bidiyo da bayanan da tawagar Khanna ta yada sun nuna wasu mutane dauke da makamai sun tare hanya a kudancin Yammacin Kogin Jordan.

Khanna ya ce bayan mazaunan yankin sun bar wurin, sojojin Isra'ila ne suka ci gaba da rufe hanyar, lamarin da ya hana su wucewa.

Ya bayyana cewa abin ya nuna irin halin da Falasdinawa ke fuskanta kullum a yankunan da Isra'ila ke mamaye da iko.

An tsare dan majalisar Amurka a Isra'ila
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: AFP

Abin da dan majalisar Amurka ya yi

Bayan an tuntubi ofishin jakadancin Amurka da kuma 'yan sandan Isra'ila, Khanna ya ce daga bisani aka ba su damar ci gaba da tafiyarsu.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ba da shawara kan gudanar da sahihin zabe a Najeriya

A nata bangaren, rundunar IDF ta ce ta samu rahoton cewa wasu fararen hula Isra'ilawa sun tare motocin baki da 'yan jarida a yankin Khirbet Zanuta.

Rundunar ta ce dakarunta sun isa wurin cikin gaggawa, suka tarwatsa wadanda suka tare hanyar tare da bude ta, tana mai jaddada cewa ba su shiga tare hanyar ba.

Ko da yake Amurka na ci gaba da kasancewa babbar kawar Isra'ila, wasu 'yan majalisar dokokinta, musamman 'yan Democrat, suna ci gaba da sukar hare-haren Isra'ila a Gaza da kuma yadda ake mu'amala da Falasdinawa.

Sojojin Isra'ila sun tsare malamin Musulunci

Mun ba ku labarin cewa sojojin Isra'ila sun tsare babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Mohammed Hussein, bayan ya jagoranci sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa.

Rahotanni sun nuna cewa bayan sojojin sun sake shi, gwamnatin Isra'ila ta hana shi shiga harabar Masallacin Al-Aqsa na tsawon mako guda.

Mahukuntan Falasdinu sun ce matakin na zuwa ne yayin da hare-hare da kutsen Isra’ila ke karuwa a wurin mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.