Ni na nada kaina a kujerar Mukarrabar Olusegun Obasanjo da kai na – Aminat Sule

Ni na nada kaina a kujerar Mukarrabar Olusegun Obasanjo da kai na – Aminat Sule

- Aminat Sule ta bada labarin yadda ta hadu da ta fara haduwa da Olusegun Obasanjo

- Sule, ‘Yar Najeriya ce da aka haifa a Ingila wanda ta zama Hadimar tsohon shugaban

- Ta ce ta yi kicibis da Obasanjo ne wajen taro, daga nan ta zama mai ba shi shawara

Wata mutumiyar Najeriya, haifaffar kasar Birtaniya, ta bada cikakken labarin yadda karfin halinta ya jawo ta zama mai ba tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawarwari.

Aminat Sule ta ce ita ta nada kan ta a matsayin Hadimar Olusegun Obasanjo da kanta. Yadda abin ya faru kuwa shi ne ta hadu da Obasanjo ne a wani lokaci da ya zo kasar Ingila.

A wancan lokaci Amina ta na gabatar da wani shiri a gidan talabijin, amma dole ta yi watsi da wannan aiki na ta saboda karancin kudi, sai ta shiga neman yadda za ta yi.

Ana haka ne sai ta samu labari Olusegun Obasanjo zai halarci wani taro da aka shirya a kan harkar siyasar Afrika a dakin taro na Chatham House da ke babban birnin Landan.

A wajen wannan taro, Aminat Sule ta yi kokarin zama inda Olusegun Obasanjo zai iya hangenta, kuma haka aka yi, ta yi ta hada ido da shi a lokacin da ake wannan zama.

KU KARANTA: Tiriliyoyi sun yi dabo daga asusun rarar man Najeriya a lokacin Obasanjo

Ni na nada kai na a kujerar Mukarrabar Olusegun Obasanjo da kai na – Amina Sule
Amina Sule da Maigidanta Obasanjo Hoto: Twitter
Asali: Facebook

A yayin da jama’a su ka karaso domin su yi hoto da tsohon shugaban Najeriyar, sai kwatsam ta fado, ta ce, ‘Hotunan sun isa haka! Za mu shiga da shi daki ya nemi ruwan sha. Zai dawo ya yi magana da ‘yan jarida nan da minti goma.'

Cif Obasanjo ya yi mamakin wannan lamari, nan ta ke ya tambayi wannan Baiwar Allah ko wanene mahaifinta, ta kuma fada masa cewa ‘Ubana ba kowa ba ne da aka sani.’

Misis Sule ta fadawa tsohon sojan ido-da-ido cewa mahaifinta gama-garin mutum ne wanda ya tsero daga Najeriya, ya dawo kasar Birtaniya domin ya samu dadin rayuwa.

A nan ne fa Sule ta yi amfani da damarta, ta ce: “To, ni ce sabuwar mai taimaka maka, zan yi aiki da kai.’ A haka kuwa ta zama Hadimar mutumin da ya mulki kasarsa sau biyu.

Sule ta ce duk da cewa da kamar wuya, ta na da burin zama ministan harkokin kasar wajen Najeriya. Ba a taba samun macen da ta rike wannan kujera a tarihin kasar ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel