Sata, munafurci da tuggu: An gurfanar da tsohon shugaban PDP a gaban kotu

Sata, munafurci da tuggu: An gurfanar da tsohon shugaban PDP a gaban kotu

An gurfanar da tsohon shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Filato, Yakubu Chocho, a gaban wata babbar kotu da ke yankin Kasuwar Nama a Jos bisa tuhumarsa da aikata rashin gaskiya, tuggu da sata.

Tsohon shugaban ya gurfana a gaban kotun ne tare da sauran wasu mutane uku da ake tuhumarsu tare da shi.

Sauran ragowar mutanen sune kamar haka; mai share-share; Helen Yakubu, maigadi; Samka Gyol, da wani kafinta; Adamu Garba.

Tsohon shugaban jam'iyyar da sauran mutane ukun sun musanta tuhumar da rundunar 'yan sanda ke mu su a gaban kotu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Helen da Samka su na aiki ne a hedikwatar jam'iyyar PDP da ke kan titin Yakubu Gowon a garin Jos lokacin da aka sace na'ura mai kwkwalwa mallakar daya daga cikin shugabannin jam'iyyar a jihar.

Bayan na'urar, an sace wasu kayayyakin mallakar Ishaku Chuntai, darektan gudanarwa na jam'iyyar PDP a jihar Filato. Kayan sun hada da wani alkalami na zinare da kayan shayi ma su tsada.

Sata, munafurci da tuggu: An gurfanar da tsohon shugaban PDP a gaban kotu
Taron jam'iyyar PDP
Asali: UGC

Dan sanda mai gabatar da kara, Daniel Longwal, ya shaidawa kotun cewa wadanda aka gurfanar sun hada baki wajen balle ofishin Chuntai tare yin awon gaba da kwamfiyutarsa, alkalamin zinare da kayan shayi da jimillar kudinsu ya kama N135,000.

Longwal ya sanar da kotun cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da aikin sauya makulli da za a yi a ofishin Chocho wajen samun damar shiga tare da yi ma sa sata.

"Mai girma mai shari'a, mutanen da aka gurafanar sun hada baki tare da tafka satar na'ura mai kwakwalwa da kudinta ya kai N125,00, alkalamin zinare na N6,000, da kayan shayi na N2,500.

"Laifin da su ka aikata ya saba da sashe na 53, 273 da 231 na kundin hukuncin aikata laifuka a jihar Filato.

DUBA WANNAN: Zargin gwamna da shugabancin Boko Haram: An hukunta gidan radiyon da su ka yada hirar Mailafia

"Sun hada baki wajen balle kofar ofishin darektan gudanarwa, Mista Ishaku Chuntai, a cikin hedikwatar jam'iyyar PDP a ranar 11 ga watan Agusta," a cewarsa.

Sai dai, dan sanda mai gabatar da kara ya gaggauta neman kotu ta daga cigaba da sauraron karar saboda wadanda ake zargi basu amsa laifinsu ba.

Lauyan da ke kare wadanda ake kara, Panshak Dakyen, ya ce yana neman belin wadanda ake zargi tunda ma su kara sun nemi a daga saurarn shari'ar

Alkalin kotun ya amince da bayar da belin wadanda ake kara a kan N50,000 kowanne mutum da kuma wakili da zai tsayawa kowannensu tare da daga sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel