Zargin gwamna da shugabancin Boko Haram: An hukunta gidan radiyon da su ka yada hirar Mailafia

Zargin gwamna da shugabancin Boko Haram: An hukunta gidan radiyon da su ka yada hirar Mailafia

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa (NBC) ta ci tarar wani gidan radiyo da ke jihar Legas Naira miliyan biyar.

NBC ta bayyana cewa an ci tarar gidan radiyon mai suna 'Nigeria Info 99.3FM' saboda yin amfani da wani shirinsu wajen yada labarai marasa tushe da kan iya haifar da hargitsi da tsana a tsakanin jama'a.

Gidan radiyon 'Nigeria Info' ne ya fara yada hirar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Obadiah Mailafia, ya yi zargin cewa wani gwamnan arewa ne ya ke shugabantar kungiyar Boko Haram.

Mailafia ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram ne ya sanar da shi hakan.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, NBC ta yi Alla-wadai da halayyar rashin kwarewar aiki da gidan radiyon 'Nigeria Info FM' ya nuna ta hanyar yada a wani shirinsa mai taken 'Morning Cros Fire'.

Gidan radiyon ya yada shirin ne da misalin karfe 8:30 zuwa 9:00 na safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Agusta.

Zargin gwamna da shugabancin Boko Haram: An hukunta gidan radiyon da su ka yada hirar Mailafia
Obadiah Mailafia
Asali: UGC

Bayan amsa gayyatar hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, tsohon gwamnan bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, ya janye ikirarin da yayi na farko.

Idan za mu tuna, a wata tattaunawa da aka yi da Mailafiya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya zargi daya daga cikin gwamnonin arewa da zama kwamandan Boko Haram a Najeriya.

DUBA WANNAN: 'Dukkan Musulman Najeriya sun aikata laifin batanci': Sakon Shekau a kan hukuncin kashe mawaki a Kano

A ranar Laraba, shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya kwatanta wannan zargi da babban al'amari da ya kamata a bincika.

Ya ce wannan ikirarin ko dai siyasa ne ko kuma wani yunkurin na sare wa gwamnonin guiwa duk da kokarin da suke yi na ganin yakar ta'addanci.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Jos, bayan amsa tambayoyi da Mailafiya ya yi, ya ce ba a fahimci zantukansa bane.

Ya yi mamakin yadda za a yanke masa hukunci daga wasu takaitattun kamai a cikin hirar da ya yi ta minti 55.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel