Wadanda su ka yi yunkurin kai wa Uzodinma hari sun shiga hannun ‘Yan Sanda

Wadanda su ka yi yunkurin kai wa Uzodinma hari sun shiga hannun ‘Yan Sanda

Dakarun ‘yan sandan Najeriya sun kama mutane 15 da ake zargin su na da hannu wajen kai hari a kan tawagar motocin gwamna Hope Uzodimma.

Jaridar Daily Trust ta ce ‘yan sanda sun bada wannan sanarwa ne a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta, 2020.

An yi yunkurin kai wa gwamnan na jihar Imo hari ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa wani barikin sojoji da ke garin Obinze domin kaddamar da wasu ayyuka.

Rahotanni sun ce gwamnan ya je Obinze ne da nufin kaddamar da wasu gidajen sojoji da gwamnatin jihar Imo ta gina a lokacin da wannan abu ya auku.

Wadannan ‘yan iskan gari dauke da gatari da bindigogi sun fito su na zanga-zanga ne a hanya, su na ikirarin su na aiki da ma’aikatar ISOPADEC ta jihar.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, ma’aikatan su na kukan an hana su albashinsu. Gwamnatin Imo ta na zargin ‘yan adawa ne su ka kitsa wannan zanga-zanga.

KU KARANTA: An yi artabu da ‘yan fasa kauri su na neman shigo da kayan da aka hana

Wadanda su ka yi yunkurin kai wa Uzodinma hari sun shiga hannun ‘Yan Sanda
Sanata Hope Uzodinma
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sanda na Imo, Isaac Akinmoyede, ya ce wadanda aka kama su na ikirarin cewa su ma’aikatan ISOPADEC ne wanda su ka yi watanni uku babu albashi.

Isaac Akinmoyede ya ke cewa sun samu wadannan mutane dauke da makamai da su ka hada da; bindiga guda, da adda. An kuma same su da tsummar rufe fuska, kwado, da kaca.

CP Akinmoyede ya ce: “Sun aukawa motocin tawagar da wata karamar bindiga ‘yar gida da addu.”

Wannan abu ya faru ne a yankin unguwar Concord a sabuwar Owerri. An yi dace babu wanda ya rasa ransa inji babban jami’in tsaron.

“Amma a sanadiyyar haka, an yi ta bugu kuma har an tarwatsa mabudan wasu daga cikin motocin da ke cikin tawagar.” inji CP.

Yanzu haka wadannan mutane da aka kama su na CID domin gabatar da bincike a kansu. Gwamnatin jihar ta ce babu yadda jami’an ISOPADEC za su rika yawo da makamai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel