An Tura Dan TikTok Gidan Yari kan ‘Barazanar’ Kashe Seyi Tinubu a Bidiyo

An Tura Dan TikTok Gidan Yari kan ‘Barazanar’ Kashe Seyi Tinubu a Bidiyo

  • An gurfanar da wani dan TikTok a Najeriya a kotun Majistare da ke Ogba a Lagos kan zargin yi wa Seyi Tinubu barazanar kisa
  • Duk da cewa matashin ya janye kalamansa tare da cewa wasa ne, gwamnatin Lagos ta ci gaba da shigar da kara a kansa
  • Kotu ta ba shi belin Naira miliyan daya da tsauraran sharudda, sannan ta umarci a tsare shi a gidan gyaran hali na Kirikiri har sai ya cika su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - An gurfanar da Ademola Abiodun, wanda aka fi sani da DJ Chicken, a gaban Kotun Majistare da ke Ogba a Lagos.

An kai matashin gidan yari bisa zargin yi wa Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Tinubu, barazanar kisa.

An daure matashi kan barazana ga Seyi Tinubu
Matashi DJ Chicken da aka tura gida yari kan barazana ga Seyi Tinubu. Hoto: @djchicken_kukuruku.
Source: Instagram

Zargin da ake yi kan DJ Chicken

Kara karanta wannan

Sakon gwamnan Kano, Abba Gida Gida ga lauyoyi game da zaben 2027

Masu gabatar da kara sun ce ana tuhumarsa da laifuka uku da suka hada da barazanar kisa, aikata abin da ka iya tayar da tarzoma, da kuma karya dokar laifukan yanar gizo, cewar Punch.

A cewar masu gabatar da kara, zarge-zargen sun samo asali ne daga wani bidiyo da DJ Chicken ya wallafa a shafukansa na sada zumunta makon da ya gabata.

An ce a cikin bidiyon ya yi kalaman da aka fassara a matsayin barazanar kashe Seyi Tinubu yayin da yake magana kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Masu gabatar da kara sun bayyana cewa kalaman sun saba da tanade-tanaden dokokin laifuffuka na Lagos da kuma Dokar Hana da Dakile Laifukan Yanar Gizo ta shekarar 2015.

An daure matashi a gidan yari kan Seyi Tinubu
Dan shugaban kasar Najeriya, Seyi Tinubu. Hoto: Seyi Tinubu.
Source: Twitter

Seyi Tinubu: DJ Chicken ya janye kalansa

Bayan bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama'a, DJ Chicken ya sake wallafa wani bidiyo inda ya janye kalamansa tare da cewa wasa ne kawai domin jan hankalin jama'a.

Ya ce ba shi da wata niyyar cutar da Seyi Tinubu, kuma kalaman na daga cikin abubuwan da yake yi wajen kirkirar abun ciki a shafukansa.

Sai dai duk da janye kalaman, gwamnatin Lagos ta ci gaba da gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifuffukan da ake tuhumarsa da su, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Kotu ta saurari karar, inda DJ Chicken ya musanta dukkan tuhume-tuhumen uku da aka karanta masa, yana mai cewa bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Mai shari'a M.F. Onamusi ta ba shi belin Naira miliyan daya tare da sharadin gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa da adadin kudi iri daya.

Kotun ta kuma shar'anta cewa daya daga cikin masu tsaya masa dole ya kasance ma'aikacin gwamnati, dayan kuma shugaba ne da aka sani a al'umma mai kadarar kasa a Lagos.

Bugu da kari, kotun ta bukaci masu tsaya masa su gabatar da shaidar biyan haraji na shekaru uku, katin LASRRA, lambar NIN da kuma takardar biyan kudin wutar lantarki ta baya-bayan nan.

Har sai DJ Chicken ya cika dukkan sharuddan belinsa, kotun ta umarci a tsare shi a gidan gyaran hali na Kirikiri, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga Agustan 2026.

Seyi ya fadi alherin Bola Tinubu

A wani labarin, an ji cewa dan shugaban Najeriya, Seyi Tinubu ya bukaci matasan Najeriya su yi hakuri tare da amincewa da shugabancin mahaifinsa.

Kara karanta wannan

"Sauran jam'iyyu suna bacci," Akpabio ya fadi yadda Tinubu zai lashe zaben 2027

Ya ce gwamnatin na kokarin gyara matsalolin da suka dade suna damun kasar duk da halin kunci na tattalin arziki.

Seyi ya nuna goyon baya ga sake zaben mahaifinsa a 2027, yana mai cewa gyare-gyaren za su amfani al’umma a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.