Kwankwason APC Ya Ari Bakin 'Yan Arewa, Ya Yi Magana kan Tikitin Tinubu da Shettima a 2027

Kwankwason APC Ya Ari Bakin 'Yan Arewa, Ya Yi Magana kan Tikitin Tinubu da Shettima a 2027

  • Jigon APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yabawa Shugaha Bola Tinubu kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki
  • Kwankwaso ya bayyana cewa wannan matakin zai kara wa jam'iyyar APC karbuwa da karfi a Arewacin Najeriya
  • Ya ce mataimakin shugaban kasa, Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan Arewa da kuma wakiltar Najeriya a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da tafiya da Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima.

Kwankwaso ya yi farin ciki da matakin Tinubu na daukar Shettima karo na biyu a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kwankwaso.
Jigon APC a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta rahoto cewa Kwankwaso, wanda shi ne Daraktan Kudi na Hukumar Raya Kogin Hadejia/Jama'are (HJRBDA), ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu/Shettima: Matsayar Kiristocin Arewa kan sake daukar Kashim a mataimaki

Matakin Tinubu ya ƙara ɗaga APC

A cewarsa, matakin da Shugaba Tinubu ya dauka ya kara wa jam'iyyar APC karfi a yankin Arewa tare da kara wa al'umma kwarin gwiwa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Ya ce zaben Shettima ya bai wa APC cikakken karfi a yankin Arewa, yana mai cewa yankin a shirye yake ya sake marawa tikitin Tinubu da Shettima baya domin samun wa'adi na biyu.

Kwankwaso ya ce:

"Matakin da shugaban kasa ya dauka shi ne mafi daɗi ga al'ummar Arewacin Najeriya. Kowane dan Arewa a shirye yake ya sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a 2027."

Kwankwaso ya taɓo 'yan adawa

Jigon na APC ya ce wannan mataki ya kawo cikas ga jam'iyyun adawa da masu adawa da sake takarar Shugaba Tinubu, kamar yadda Independent ta ruwaito.

Ya bayyana Shettima a matsayin daya daga cikin ginshikan nasarar siyasar gwamnatin Tinubu a Arewa, yana mai yabawa kokarinsa na hada kan al'ummar yankin.

Kara karanta wannan

Shettima ya kai wa Tinubu ziyara bayan APC ta tabbatar da shi a tikitin 2027

Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yana jagorantar taro a Aso Rock Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

An yaba wa Kashim Shettima

Kwankwaso ya kuma yabawa gudunmawar da Shettima ke bayarwa wajen tafiyar da mulki, yana mai cewa ya taka rawar gani wajen karfafa hadin kan Najeriya tare da wakiltar Shugaba Tinubu yadda ya kamata a tarukan kasa da kasa.

Ya ce:

"Mun ga yadda Kashim Shettima ke aiki tukuru wajen tabbatar da hadin kan Arewa da ma Najeriya baki daya. Haka kuma mun ga yadda yake wakiltar Shugaban Kasa cikin kwarewa a dandalin duniya."

Ndume ya taya Kashim Shettima murna

An ji cewa Sanata Ali Ndume ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar sake fi0towa a matsayin abokin takarar Bola Tinubu a 2027.

Ya ce sake zaɓen mataimakin shugaban ƙasa a matsayin abokin takarar Shugaba Tinubu a zaɓe na gaba zai ƙara wa jam’iyyar APC ƙarfi wajen neman samun nasara.

Sanatan ya ce matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka ya nuna hangen nesa, dabarun shugabanci da kuma cikakken amincewa da lƙwarewa, biyayya da sadaukarwar Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262