"Ku Taimaka": Remi Tinubu Ta Roki Davido da Sauran Manyan Mawaka a Najeriya
- Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci Burna Boy, Davido da Asake su kafa gidauniyoyi domin taimaka wa talakawa
- Ta ce Najeriya na da attajirai da dama, amma ya kamata su ƙara ba da gudummawa saboda nauyin da ke kan gwamnati
- Uwargida shugaban kasar ta kuma sanar da tallafin Naira miliyan 100 ga ƙananan ƴan kasuwa 2,000 a jihar Kogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lokoja, Kogi - Uwargidan shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga fitattun mawakan Afrobeats, Burna Boy, Davido da Asake, da su kafa gidauniyoyi domin taimaka wa marasa galihu a Najeriya.
Remi Tinubu ta ce Najeriya na da attajirai masu yawa, amma akwai buƙatar su ƙara tallafa wa mabukata saboda nauyin da ke kan gwamnati yana da yawa.

Kara karanta wannan
"Ku yaki 'yan bindiga"; Tsare tsohon malami ya jawo abin magana ga gwamnatin Katsina

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce Remi Tinubu ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026 a Lokoja, jihar Kogi, yayin ƙaddamar da shirin bankin abinci na al'umma na ƙasa.
Oluremi Tinubu ta ce lokaci ya yi da masu hannu da shuni za su mayar da hankali wajen taimakon al'umma.
Ta yabawa Akon, ta yi kira ga mawakan Najeriya
Uwargidan shugaban ƙasar ta kawo misalin fitaccen mawaki Akon, inda ta ce ya shahara wajen ayyukan jin ƙai ta hanyar gidauniyarsa, jaridar The Punch ta kawo rahoton.
"Najeriya ƙasa ce mai albarka. Muna da attajirai da yawa, amma abubuwan da muka fi ba muhimmanci sun bambanta. Ina ganin lokaci ya yi da za mu fara taimaka wa mabuƙata a ƙasarmu."
"Ina kira ga matasanmu da ke harkar nishaɗi. Burna Boy, Asake, Davido da sauran su, muna son ganin kowannenku yana da gidauniya da ke taimaka wa talakawa da dukiyar da Allah Ya ba ku."
- Sanata Oluremi Tinubu
Ta kuma ce mallakar motoci masu tsada kamar Maybach da Rolls-Royce abu ne mai kyau, amma hakan bai kamata ya hana masu kuɗi taimaka wa mabukata ba.
Ta yabawa sana'o'in hannu
Oluremi Tinubu ta ce bai kamata a raina halal ɗin sana'a ba, tana mai jaddada cewa masu sayar da barkono, kayan lambu, kubewa, gyada, ƙuliƙuli da sauran ƙananan sana'o'i suna gudanar da rayuwa cikin mutunci.
Ta ba da labarin wani matashi da ya kammala jami'a amma ya fara sana'ar sayar da kosai bayan ya rasa aikin yi.
A cewarta, an taimaka masa ba tare da bayyana sunanta ba, aka faɗaɗa kasuwancinsa, kuma yanzu yana ɗaukar ma'aikata 12 da ke aiki a ƙarƙashinsa.
Uwargidan shugaban kasar ta ce wannan misali ya nuna cewa bai kamata mutane su raina kowace sana'a ta halal ba.
An ware Naira miliyan 100 ga ƙananan ƴan kasuwa
Da take magana kan shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki a jihar Kogi, Oluremi Tinubu ta sanar da cewa shirin Renewed Hope Initiative (RHI) ya bayar da gudummawar Naira miliyan 100 ga uwargidan gwamnan jihar Kogi kuma mai kula da shirin a jihar.
Ta bayyana cewa za a yi amfani da kuɗin wajen tallafa wa ƙananan ƴan kasuwa 2,000, inda kowannensu zai karɓi Naira 50,000 domin ƙara jari a kasuwancinsa.

Source: Facebook
Uwargidan shugaban ƙasar ta yaba wa waɗanda suka amfana da tallafin, tana mai cewa ta ji daɗin ganin wasu mata sun tarbe ta da kayayyakin sana'arsu, abin da ta ce ya nuna sun fahimci manufar shirin.
Ta ce hakan ya tabbatar da cewa saƙon ƙarfafa ƙananan sana'o'i ya isa ga al'umma, duk da yadda wasu ke fassara shirin.
Remi Tinubu ta yi girbi a gona
A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta sake girbe kayan lambu daga gonarta.
An yi gonar ne kimanin shekaru biyu da suka gabata domin inganta samar da wadataccen abinci a Najeriya ta hanyar shirin samar da abinci a gidaje.
Asali: Legit.ng

