China: Macizai Masu Hadari Sun Fara Kisa da Ambaliya Ta Yi Kaca Kaca da Gonakinsu

China: Macizai Masu Hadari Sun Fara Kisa da Ambaliya Ta Yi Kaca Kaca da Gonakinsu

  • Daruruwan macizai, ciki har da wanda ake kira da Cobra, sun afka wa mutane bayan ambaliya ta lalata gonakin da ake kiwonsu a China
  • Rahotanni sun nuna cewa an kai mutane da dama asibiti bayan macizai sun sare su, yayin da mutum guda ya rasa ransa
  • Mummunar ambaliyar ruwan da aka yi ta kashe akalla mutum 38 tare da tilasta wa dubban mutane barin gidajensum a China

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

China - Daruruwan macizai, ciki har da macizai masu dafi irin na Cobra, sun tsere daga gonakin kiwonsu bayan ambaliyar ruwa ta mamaye yankunan kudancin kasar China.

An ruwaito cewa gonar kiwon macizai da ke birnin Hengzhou, a yankin Guangxi Zhuang, ta lalace bayan sakamakon ambaliyar ruwa da guguwar Typhoon Maysak ta haddasa.

Ambaliya.
Ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan kasar China Hoto: STR
Source: Getty Images

Mutane sun fara kama macizai a China

Kara karanta wannan

Jirgin sama ɗauke da mataimakiyar shugaban ƙasa da wasu mutum 8 ya yi hatsari

Guardian ta rahoto cewa wani bidiyo da ya bazu ya nuna yadda wasu mazauna yankin ke amfani da fatsa ta kamun kifi wajen kama macizan, yayin da aka ga wani Cobra ya daga kansa daga cikin ruwa.

Rahotanni sun ce daga cikin macizan da suka tsere akwai macizan ruwa, King Ratsnake da kuma Cobra.

Cobra ya sari wani mutum

Wani mutumi da ke kwance a asibiti yana jinya ya shaida wa tashar CNN cewa Cobra ya sare shi lokacin da yake kwashe tarkace a benen gidansa.

Ya ce:

"Daruruwan macizai ne suka tsere lokaci guda. Ni da kaina na ga biyar zuwa shida."

Likitan da ke kula da masu fama da cizon maciji ya tabbatar da cewa an kai mutane da dama asibiti tun bayan fara ambaliyar.

Ambaliyar uwa ta yi barna a China

Ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a yankin Guangxi, inda ta mamaye kauyuka da dama bayan wasu madatsun ruwa biyu suka cika tare da ballewa.

Rahotanni sun ce akalla mutum shida sun mutu, yayin da sama da mutane 50,000 suka tsere daga gidajensu. Har yanzu ana neman wasu mutum shida da suka bace.

Kara karanta wannan

Bayan an shafe shekaru ba ko digo, gwamnati ta farfaɗo da matatar ruwa a Kano

Xi Jinping.
Shugaban kasar China, Xi Jinping a wurin taro fa wasu jami'an gwamnatinsa Hoto: China Pool
Source: Getty Images

Shugaba Xi Jinping ya ba da umarnin ceto

Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya umarci hukumomi da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukan ceto yayin da ambaliya da sauran matsanancin yanayi ke ci gaba da addabar yankuna daban-daban.

Hukumomin Hengzhou sun tabbatar da cewa ambaliyar ta lalata gonakin kiwon macizai, lamarin da ya sa macizai masu dafi suka tsere tare da kai hari ga wasu mazauna yankin.

Ambaliya ta yi ajalin mutane a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa ruwan sama mai tsanani da ha haddasa ambaliya ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 12 a yankuna daban-daban na kasar Saudiyya.

Ruwan saman da ya janyo ambaliya da kuma katse hanyoyi, sannan hukumomin ceto suka bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da kai agaji ga al’ummomin da lamarin ya shafa.

Rahotanni sun nuna cewa an kafa kwamitoci daban-daban domin tantance adadin barnar da ambaliyar ta yi , musamman a yankunan da ruwan sama mai karfi ya fi shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262