Oshiomhole ya zargi gwamnonin APC da kokarin kai shi kasa

Oshiomhole ya zargi gwamnonin APC da kokarin kai shi kasa

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, a ranar Litinin a Abuja.

Ya zargi gwamnonin APC da amfani da darakta janar na kungiyar, Salihu Lukman, don kai shi kasa.

A yayin martani ga wani hasashe da kungiyar ta yi na cewa zai koma shugabancin jam’iyyar, Oshiomhole ya zargi gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi, da nada Lukman a matsayin shugaban kungiyar shi kadai.

Ya sanar da manema labarai cewa ba zai shiga kazamin fadan da Lukman ke nemansa da shi ba.

Oshiomhole ya zargi gwamnonin APC da kokarin kai shi kasa
Oshiomhole ya zargi gwamnonin APC da kokarin kai shi kasa
Asali: Depositphotos

"Abinda basu gane ba shine ba kujerar shugaban jam'iyyar bace ta sa na zama abinda na zama. Na yi aiki a masana'antar masaka inda na zama babban sakataren masana'antu na dukkan Najeriya kuma na zama shugaban kungiyar kwadago.

"Babu wani kauye da zan shiga jama'a basu sanni ba kuma hakan nayi amfani da ita wurin wuce iyayen gidansa a Edo.

"A don haka ni bana iya mayar da martani ga masu surutu kuma wadanda kungiyar gwamnonin ce ta daukesu aiki.

"Ya yi takarar majalisar wakilai a Makarfi ya fadi. Ya yi takara da gwamna El-Rufai kuma ya fadi yayin zaben fidda gwani kuma ya sha kaye kafin Fayemi ya zabesa."

A baya mun ji cewa darakta janar na kungiyar gwamnonin APC, Dr Salihu Lukman, ya zargi cewa akwai shirin mayar da Adams Oshiomhole tsohuwar kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin binciken Kwankwaso

Ya yi ikirarin cewa akwai kokarin da ake yi don zagon kasa ga kwamitin rikon kwarya na Mai Mala Buni.

DG Lukman a wani bayani da yayi a kan kwamitin rikon kwaryan, ya ce: "komai ana yin shi ne don ganin an juya siyasar cikin gida don samun yadda Oshiomhole zai haye kujerar shugabancin jam'iyyar."

Lukman, wanda babban mai adawa ne da salon Oshiomhole, ya ce daga cikin wani bangare na kokarin shine amfani da zaben Edo wajen cin zarafin shugabannin APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng