Lauyan da ke kare Ibrahim Magu ya aikawa kwamitin Ayo Salami takardar korafi
Mista Wahab Shittu, Lauyan da ya tsayawa tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya aika takarda ga kwamitin bincike na Ayo Salami.
Lauyan ya na zargin wannan kwamiti na shugaban kasa da laifuffuka iri-iri, daga ciki har da sabawa dokar aiki, da kuma tauyewa Mista Ibrahim Magu hakkinsa.
An aika wannan takarda zuwa ga shugaban kwamitin binciken hukumar EFCC ne ranar 11 ga watan Agusta, 2020 kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto.
Shittu ya bayyana lamarin da abin takaici da damuwa bayan ganin aikin kwamitin ya rikida daga karbar hujjoji zuwa cikakken bincike wanda hakan ya sabawa doka.
Yadda aikin kwamitin ya zama wani abu dabam ya ci karo da dokar bincike ta kasa ta shekarar 2004 inji lauyan.
A cewar lauyan, tun da aka fara wannan bincike na musamman ba a gayyaci tsohon shugaban hukumar ta EFCC gaban kwamitin ba sai da aka shafe kwanaki 35 ana aiki.
A wasikar da aka aikawa Ayo Salami da ‘yan kwamitinsa, lauyan ya na mai sukar yadda ake gudanar da binciken a asirce ba tare da an bar kowa ya san abin da ake ciki ba.
KU KARANTA:
Bugu da kari, a lokuta daban-daban a watan da ya gabata, an hana Ibrahim Magu da lauyansa bayyana a gaban kwamitin binciken, a cewar Mista Shittu.
Ibrahim Magu ta bakin lauyan na sa ya ce ba a shi damar yi wa wadanda su ka hallara gaban kwamitin tambayoyi domin a tabbatar da gaskiyar hujjojin da su ka gabatar ba.
Haka zalika ba a neman masu bayani a gaban kwamitin da su rantse, wanda wannan ya ci karo da sashe na 5(b) na dokar bincike na 2004 inji lauyan.
Wani abin kokawa da binciken shi ne shiga sharo ba shanu da kwamitin ya ke yi da kuma rashin tantance wa’adin aikin kwamitin wanda bai kamata ya zarce kwanaki 45 ba.
Korafi na karshe da ake yi shi ne kwamitin ya na sauraron lamarin da su ke gabankotu a halin yanzu, wannan ya na nufin Salami ya na cusa baki kan abin da ya fi karfinsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng