Shugabancin kasa a 2023: Matasan Ohanaeze sun bayyana mutum 2 da suka zaba

Shugabancin kasa a 2023: Matasan Ohanaeze sun bayyana mutum 2 da suka zaba

- Wasu kungiyoyin matasan Ibo sun bayyana mutum biyu da suka zaba daga yankin kudu maso gabas don shugabancin kasa a 2023

- Kungiyoyin sun sanar da hakan ne a wata takarda bayan taron hadin guiwa da aka yi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi

- Matasan sun bayyana ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu da Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a matsayin zabinsu

Wasu kungiyoyin gamayya na matasan Ibo da ke fadin kasar nan sun amince da wasu 'yan siyasa biyu daga yankin kudu maso gabas don shugabancin kasa a 2023.

A wata takardar da kungiyoyin matasan suka fitar bayan taron hadin guiwar a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a ranar Asabar, 15 ga watan Augusta, sun bayyana zabinsu.

Sun bayyana ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu da Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, a matsayin wadanda suke so su gaji Muhammadu Buhari, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda takardar ta sanar, sun bayyana Onu da Umahi a matsayin 'yan takararsu saboda yanayin shugabancin da suka bayyana.

Shugabancin kasa a 2023: Matasan Ohanaeze sun bayyana mutum 2 da suka zaba
Shugabancin kasa a 2023: Matasan Ohanaeze sun bayyana mutum 2 da suka zaba Hoto: Premium Times/Cfr.org/Blueprint.ng
Asali: UGC

Matasan sun bayyana Umahi a matsayin gwamnan da ya zama gwarzo a gwamnonin yankin kudu maso gabas sakamakon irin kayayyakin more rayuwar da ya yi a jihar da.

A dayan bangaren, sun bayyana Onu a matsayin dan siyasan da ya taka rawar gani wurin majan jam'iyyun siyasa uku wanda hakan ya bada jam'iyyar APC.

Kamar yadda suka ce, ministan yana da nagartar shugabanci wanda yayi kuma an gani ba tare da wata alaka ko zargin rashawa ba.

KU KARANTA KUMA: Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani

"Wadannan sune mutanen da muke fatan su shugabanci kasar nan kuma su matasan Ibo ke so," kungiyoyin ta ce.

Sun yi bayanin cewa, sauran da suka cancanci shugabancin kasa a yankin suna fuskantar zargin rashawa.

A gefe guda, mun ji cewa majalisar dattawan Biyafara, a jiya, ta yi watsi da jawabin kungiyar Ohanaeze Ndigbo da wasu yan siyasan kabilar Igbo cewa shugabancin kasan Najeriya suke a 2023 ba ballewa daga Najeriya ba.

Majalisar ta bayyana matsayarta ne a takardar da ta saki bayan ganawar wata-wata karkashin jagorancin shugabanta, Cif Solomon Ordu Chukwu, da aka saba yi a Owerri, babbar birnin jihar Imo.

Dattawan sun bayyana cewa abinda kabilar Igbo ke nema yanzu shine sauyin kasar gaba daya, ba sauyin wani mutum daya ko shugaba ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel