Mansurah Isah Ta Kwancewa Rarara Zani a Kasuwa, Ta Bar Kungiyar Tallata Tinubu
- Jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta gargadi mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara da matarshi Aisha Humairah
- Hakan na zuwa ne bayan ta sanar da ficewa daga tafiyar Dauda Rarara da ke amfani da ita wajen tallata shugaba Bola Tinubu
- Mansurah Isah ta bayyana cewa ta fito ta yi magana ne a bisa dole ba domin tana so ba, saidai saboda Rarara ya karya alkawari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Baraka na cigaba da bulla a tsakanin 'yan fim din Kannywood masu tallan Bola Tinubu a karkashin kungiyar Dauda Kahutu Rarara.
Jaruma Mansurah Isah da ta yanke alaka da kungiyar Dauda Rarara ta fito da wasu maganganu da ta ce ta yi su ne a bisa dole.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa jarumar ta yi maganganun ne a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook bayan sabani da Rarara.

Kara karanta wannan
APM ta ɗauko batun yadda Bola Tinubu ya kashe kuɗin tallafin mai da ya cire a Najeriya
Mansurah ta zargi Rarara
Mansurah Isa ta yi martani ne inda ta ce idan aka taba ta, za ta taba duk wanda ya mata ba daidai ba, ba tare da jin tsoro ko shakka ba.
Ta bayyana cewa ta san duk abubuwan da suka faru da suka sanya ta barin tafiyar kuma za ta fito da komai idan ba a kiyaye ta ba.
Mansurah ta zargi Dauda Rarara ta tara wasu mutane da ke zagin duk wanda ya caccake shi, amma sai dai ta ce tana da digiri a kimiyyar siyasa kuma ba ta tsoro:
"Bana son in yi rigama, kuma ba tsoron uban kowa nake ba, ban shakkar kowa, kuma kowa ya sani."
Mansurah ta kame baki a baya
Yayin da ta fara magana a kan abubuwan da suka faru a baya, jarumar ta ce ta kame bakinta ne a baya domin ta yi alkawarin yin shiru.
Ta bayyana cewa manyan 'yan jarida da kafafen yada labarai kamar BBC, DW da sauransu sun nemi su yi magana da ita amma ta ki.
A kan haka ta gargadi Rarara da matar shi su kiyayi kansu daga shiga lamuranta, tana cewa siyasar za ta wuce gaba daya a wata shida masu zuwa.
Ta ce idan kuwa suka ki kame bakinsu, za ta fito da dukkan abubuwan da suka faru, domin sun san muminai da munafukai a tafiyar.
Dalilin rabuwar Rarara da Mansurah
Yayin da take bayani kan abin da ya raba su, Mansurah Isah ta ce an samu wata dama ce a baya, sai ta nemi mika ta ga dukkan 'yan Kannywood.
A cewarta, Rarara ya ce mata hakan ba mai yiwuwa ba ne, ya ce yan kungiyarsa ta Triple R ne kawai ya kamata su amfani da wani abu da aka samu daga gwamnati.

Source: Twitter
Ta bayyana cewa hakan yasa ta ce ba zai yiwu ba, ta kara da cewa Rarara ya nemi ta zabi tafiyar shi ko ta dan shugaban kasa, inda ta ce ta zabi ta dan shugaban kasa.
An ba su rarara miliyoyi
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Dauda Kahutu Rarara ta samu kudi har Naira miliyan 500 domin tallata Bola Tinubu a Arewa.
Sakataren kungiyar Triple R, Ahmad Bifa ne ya bayyana cewa tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ne ya ba su makudan kudin.
Bifa ya bayyana haka ne yayin da wasu 'yan Kannywood suka fara caccakar tafiyar Rarara suna barranta da ita saboda wasu matsaloli.
Asali: Legit.ng

