Gwamnatin Jihar Ribas ta balle daga shirin daukar Ma’aikata 774, 000 aiki - Awortu

Gwamnatin Jihar Ribas ta balle daga shirin daukar Ma’aikata 774, 000 aiki - Awortu

Gwamnatin jihar Ribas ta fita daga shirin zaben matasan da gwamnatin tarayya za ta rabawa kananan ayyuka na masu karamin karfi a Najeriya.

Mai taimakawa gwamnan Ribas Nyesom Wike a kan sha’anin NDDC, Erastus Awortu, ya bada wannan sanarwa a ranar Laraba, 12 ga watan Agusta, 2020.

Erastus Awortu ya aikawa karamin ministan kwadago da aikin yi na kasa, Festus Keyamo takarda ya na bayyana dalilin gwamnatin Ribas na daukar wannan mataki.

Hadimin gwamnan ya yi kukan cewa kwamitin zaben wadanda za a ba wadannan ayyuka da Dr. Innocent Barikor sun maida tsarin tamkar na ‘yan jam’iyyar APC.

Mista Awortu ya fadawa Festus Keyamo (SAN) a wasikar ta sa cewa Innocent Barikor ya sabawa ka’ida wajen zakulo wadanda za su yi wannan aiki daga jihar Ribas.

“Ina cikin kwamitin gwamnatin jihar Ribas na masu zakulo wadanda za a ba aiki, ina so in sanar da kai game da tsabar kaucewa ka’ida da siyasantar da lamarin daukar aikin da aka yi a jihar.”

“Daga sharudan farko da ka bada daga ofishinka bayan kaddamar da shirin, ka bayyana yadda za a raba ayyukan bayan an warewa ‘yan siyasa da ke kan kujerun mulki kasonsu.”

KU KARANTA: Gwamnan Benuwai ya na so Gwamnati ta kyale a rika amfani da bindiga

Gwamnatin Jihar Ribas ta balle daga shirin daukar Ma’aikata 774, 000 aiki - Awortu
Minista Festus Keyamo SAN
Asali: Twitter

“Bayan an cire kason masu mulki a ragowar mutane 1, 000 daga kananan hukumomi, kowane daga cikin ‘yan kwamitin zai samu rabon kujeru 20 saboda mutanen da ya ke wakilta.”

“Daga nan sai wanda da ke cikin masu zakulo wadanda za a rabawa aikin ya kawo sunayen wadanda za a zaba daga karamar hukuma zuwa ga shugaban kwamitin bayan wani lokaci.”

A cewar Erastus Awortu, a halin yanzu Barikor sun saki layi wajen wannan aiki.

“Shugaban kwamitin da sakatarensa da ‘yan jam’iyyar APC da ke cikin kwamitin sun warewa wasu tsirarru kujerun mutane 100 daga kowace karamar hukuma.” Inji Hadimin gwamnan.

An ba kungiyar CAN kujeru 10, majalisar kolin addinin musulunci ta samu 5, sarakunan gargajiya sun samu 10. Hadimin ya ce a matsayinsa na wakilin gwamna bai samu komai ba.

Shugaban kwamitin ya ce za a raba ragowar kujeru 775 na kowace karamar hukuma ne ga ‘yan jam’iyyar APC kawai, wannan ya sa Awortu ya ce ba za su shiga cikin wannan tsari ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng