Ba gudu ba ja da baya, 'yan kudu ne zasu karbi shugabancin kasar a 2023 - El-Rufai

Ba gudu ba ja da baya, 'yan kudu ne zasu karbi shugabancin kasar a 2023 - El-Rufai

- Gwamna Nasir El-Rufai, ya ce babu gudu babu ja da baya a kan goyon bayan komawar shugabancin kasa a 2023 zuwa yankin kudancin Najeriya

- El-Rufai ya ce yarjejeniyar ce aka yi, cewa bayan Muhammadu Buhari, shugabancin kasa zai koma kudu

- Ya ce bai taba cewa ba zai goyi bayan 'yan arewa ko 'yan kudu ba, amma dole ne shugabanci ya koma kudu a 2023 duk da kuwa kundin tsarin mulkin APC bai gindaya hakan ba

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Lahadi ya ce babu gudu babu ja da baya a kan goyon bayan komawar shugabancin kasa a 2023 zuwa yankin kudancin Najeriya.

El-Rufai, wanda ya yi bayani ga gidan talabijin na Channels, ya ce sakamakon yarjejeniyar da aka yi, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugabancin kasa zai koma kudu.

Kamar yadda yace, ko jam'iyyar PDP na da wannan yarjejeniyar ta karba-karba, wanda hakan ne yasa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da marigayi Umaru Yar'adua suka yi mulki.

Ba gudu ba ja da baya, 'yan kudu ne zasu karbi shugabancin kasar a 2023 - El-Rufai
Ba gudu ba ja da baya, 'yan kudu ne zasu karbi shugabancin kasar a 2023 - El-Rufai Hoto: PM News
Asali: UGC

Ya ce bai taba cewa ba zai goyi bayan 'yan arewa ko 'yan kudu ba, amma dole ne shugabanci ya koma kudu a 2023 duk da kuwa kundin tsarin mulkin APC bai gindaya hakan ba.

"Bayan shugaba Buhari, abinda ya fi wa yankin arewaci shine bai wa 'yan kudu goyon baya. Ban yarda da siyasar yanki ba amma wannan ne ra'ayina. Muna da wannan shirin, kuma dole mu kiyaye.

KU KARANTA KUMA: Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Fadar shugaban kasa ta yi martani

"Ban yarda cewa wani yanki na Najeriya ba zai dawwama a mulki ba. Muna da fahimta, don haka mu kiyaye. A 1998, an tsayar da cewa mulki ya tafi yankin kudu maso yamma.

"A 2023, na yarda dukkan jam'iyyun siyasa su kawo 'yan takara daga yankin kudu," yace.

A wani labarin, wasu kungiyoyin na matasan Ibo da ke fadin kasar nan sun amince da wasu 'yan siyasa biyu daga yankin kudu maso gabas don shugabancin kasa a 2023.

Sun bayyana ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu da Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, a matsayin wadanda suke so su gaji Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel