Bayan Saukar Pantami a Filin Jirgi, Gwamnatin Gombe Ta Yi Barazanar Bincike
- Hukumar filin jirgin saman Gombe ta fitar da gargadi mai tsanani bayan zargin amfani da wajen domin harkokin siyasa ba bisa doka ba
- Rahoto ya nuna cewa hukumar ta ce filin jirgin sama wurin tsaro ne da doka ta kare, kuma ba a yarda da duk wani aiki na siyasa a cikansa ba
- Ta yi gargadin ne bayan dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami ya samu tarba a filin jirgin saman da yammacin ranar Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gombe - Hukumar filin jirgin saman Gombe ta fitar da sanarwa a ranar Juma'a, 10 ga watan Yulin 2026, tana mai gargadin duk wanda zai yi amfani da filin don harkokin siyasa.
Sanarwar ta zo ne bayan wani lamari da ya faru a filin, inda ta ce wasu mutane sun shiga yankin da aka ware domin ayyukan yau da kullum.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji suka kutsa dajin Oyo, suka gwabza da 'yan bindiga yayin ceto dalibai

Source: Facebook
A sakon da ta fitar a Facebook, hukumar ta ce bayan shigarsu, sai suka fara lamuran siyasa ta hanyar yabawa wani mutum a bainar jama'a.
Gargadin gwamnatin Gombe
Hukumar ta bayyana a fili cewa filin jirgin saman Gombe wurin da ake kula da shi ne sosai, kuma ba ya yarda da duk wani aiki na jam'iyyun siyasa, ko taro, ko gangami, ko tallafawa mai neman takara ba.
Ta kara da cewa duk wanda aka ba izinin shiga filin, ko ma'aikaci ne ko bako, dole ya yi abin da aka ba shi izini ne kawai, ba wai wani abu na siyasa ba.
Hukumar ta yi bayanin cewa duk wanda ya keta wannan doka za ta dauki mataki a kan shi a matsayin wanda ya karya ka'idojin filin.
Ta ce:
"Haka kuma, filin jirgin ba ya goyon baya, amincewa, ko yarda da gudanar da kamfen na siyasa, gangamin siyasa, zanga-zanga, bayyana goyon baya ga wani ɗan siyasa, ko wata irin harkar siyasa ta ɓangaranci a cikin harabarsa, musamman a yankunan gudanar da ayyukan jiragen sama da aka takaita shiga."

Source: Facebook
Batun yin bincike a filin jirgi
Hukumar ta sanar da cewa tana gudanar da bincike kan yadda abin ya faru, domin a gano irin rawar da kowane mutum ya taka.
Ta ce duk wanda aka samu da laifin taimakawa ko shiga cikin wannan hali zai fuskanci hukunci bisa dokokin da suka dace, ba sani ba sabo.
Sanarwar ta ce:
"A halin yanzu, hukumar gudanarwa tana ci gaba da binciken yadda lamarin ya faru. Duk wanda aka tabbatar ya taimaka, ya ƙarfafa, ko ya shiga cikin wannan rashin da'a, za a ɗauki matakan ladabtarwa da suka dace a kansa bisa ga ƙa'idojin da ake aiki da su,"
Gwamnati ta gargadi Obi
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gargadi dan takarar NDC, Peter Obi bayan korafi a filin jirgin sama.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa Obi ya yi korafi a kan abin da ya faru a Abuja, amma bincike ya gano cewa ba shi da gaskiya.
A kan haka, Keyamo ya bukaci Obi ya fito fili ya bayar da hakuri kuma ya biya tarar da aka daura masa ko kuma FAAN ta dauki matakin da ya dace.
Asali: Legit.ng
