Siyasar Najeriya
A ranar uku ga watan Nuwamba ne Amurkawa zasu kada kuri'unsu ga daya daga cikin 'yan takara biyu; Donald Trump, da Sanata Joe Biden, da ke neman kujerar shugaba
Zanga-zangar lumunar da aka fara a wasu jihohin ta canza salo, ta koma rikici. Shugaban kasa ya ba Ministoci umarni su je gida su duba wannan lamarin #EndSARS.
Gwamna Fintiri ya saka dokar ta baci a jihar Adamawa bayan matasa sun fake da zanga-zangar ENDSARS domin cigaba da tafka barna a ma'adanan gwamnati da gine-gine
Za a fara bin gidajen Bayin Allah domin bankado barayi a jihar Adamawa. Wasu tsageru sun shiga dakunan ajiya sun yi awon-gaba da dukiyar gwamnati a makon jiya.
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya goyi bayan kiran da matasa ke yi a kan cewa ya kamata wanda zai gaji shugaban kasa Buhari ya fito daga kudu maso gabas.
Karar da aka kai tsohon gwamna Bola Tinubu ta gamu da cikas din farko a kotu. Takardun karar Bola Tinubu sun kone kurmus a cikin kotu inji Lauya mai korafi.
Sanata Dino Melaye ya ce an yi hayar ‘Yan daba su kona gidansa a Aiyetoro-Gbede a jiha Kogi, ya ce burinsu shi ne su ruguza gidan, amma Ubangiji ya yi da rabo.
Gwamnan Jihar Kogi ya ce zanga-zangar #EndSARS ta na alaka da zabe mai zuwa na 2023. Yahaya Bello ya bugi kirji, ya ce akwai siyasa a zanga-zangar #EndSARS.
A makon da ya wuce, an samu wasu ‘Yan iskan Gari da su ka auka wa Sakatariyar APC a Jihar Delta. Bata-garin sun yi yunkurin ruguza Hedikwatar Jam’iyyar APC.
Siyasar Najeriya
Samu kari