‘Dalilin da Ya Sa Mutane ba Su Son Takarar Pantami, Shehu Buba’: Sheikh Adam

‘Dalilin da Ya Sa Mutane ba Su Son Takarar Pantami, Shehu Buba’: Sheikh Adam

  • Mutane musamman malamai na ci gaba da bayyana goyon baya ga Farfesa Ali Pantami a takarar gwamnan Gombe
  • Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya ce Pantami na fuskantar adawa ne saboda kasancewarsa malamin addini
  • Malamin ya ce Sanata Shehu Buba yana haɗa kan Musulmi da Kirista cikin adalci, inda ya bukaci nagartattun mutane su shiga siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana ci gaba da samun masu goyon bayan Farfesa Ali Pantami yayin da ya ke neman takarar gwamnan Gombe.

Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yabawa Ali Pantami da Sanata Shehu Buba da ke jihar Bauchi kan takarar da suke nema.

Malami ya fadi alherin Pantami da Sanata Shehu Buba
Farfesa Isa Ali Pantami, Sheikh Ishaq Adam Ishaq da Sanata Shehu Buba. Hoto: Sheikh Barr. Ishaq Adam Ishaq, Professor Isa Ali Pantami/Facebook.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani bidiyo da wakilin Legit Hausa ya samu wanda Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sakon gwamnan Kano, Abba Gida Gida ga lauyoyi game da zaben 2027

Malami ya goyi bayan takarar Farfesa Pantami

Malamin ya ce abin takaici ne yadda ba a goyon bayan Pantami da Shehu Buba saboda kyawawan halayen da suke da shi.

A cewara:

"Akwai mutane da suka fito takara, kuma na gari, akalla ana tsammanin za su kwatanta adalci kamar Farfesa Isa Ali Pantami.
"Kowa ya sani lokacin da yake minista ai ya kwatanta, daman damuwar mu shi ne idan barna 100 ce, a samu wanda zai rage 20.
"Wani ma idan ya zo ya rage 20, a haka a hankali, a hankali wani ya rage mana har mu dawo ba mu da matsala."
Shehi ya fadi dalilin da ya sa ake yi wa Pantami adawa
Babban malamin Musulunci daga Kano, Sheikh Ishaq Adam Ishaq. Hoto: Sheikh Barr. Ishaq Adam Ishaq.
Source: Facebook

Dalilin adawar da Pantami ke fuskanta

Malamin ya bayyana cewa malam Pantami na fuskantar adawa da kiyayya saboda kawai shi malami ne wanda hakan ba adalci ba ne.

Ya kuma bayyana yadda Sanata Shehu Buba ke hada kan al'ummarsa ba tare da bambancin addini ba.

"Farfesa Ali Pantami babu abin da ya ke fuskanta sai adawa da kiyayya saboda malamain addini ne, idan za a yi masa adalci, a cire Kur'ani da hadisin da yake da shi, Farfesa ne a ilimin kwamfuta.

Kara karanta wannan

Yadda Al Jazeera ta ba hadimin Tinubu hakuri a asirce kan wata hira da suka yi

"Yanzu a Bauchi muna da irinsu Shehu Buba, abin da zai burge ka da shi mutum ne wanda bai da bambancin addini tsakanin Musulmi da Kirista.
"Za ka ga a cikin masoyansa akwai Musulmi da Kirista saboda yana masu adalci, irin wadannan ka ga ba a so su yi, saboda sun hada kan jama'a.
"Idan zaka jagoranci Najeriya, dole ka kula da hakkin Kiristoci saboda suna da hakki a dokar kasa, shi yasa Pantami da Buba muke masu addu'ar Allah ya sa su yi nasara."

- Sheikh Ishaq Adam Ishaq

A karshe, malamin ya shawarci mutanen kirki da su shiga siyasa domin tabbatar da kawo sauyi a cikin al'umma.

Malamin ya fadi hukuncin irinsu Turji a Musulunci

An ji cewa Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi watsi da ra'ayin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa Musulunci ya umurci a yake su.

Malamin ya bayyana cewa addini da dokar kasa duk sun amince a kashe su ko a hukunta su matukar suna ci gaba da barna.

Ya kalubalanci masu cewa ‘yan bindiga sun fi karfin jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati na da ikon kawo karshen su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.