Ginin Majalisar Gombe Ya Rufta kan Mutane, Gwamnati Ta Dauki Matakin Gaggawa

Ginin Majalisar Gombe Ya Rufta kan Mutane, Gwamnati Ta Dauki Matakin Gaggawa

  • Gwamnatin Gombe ta ba da umarnin gudanar da binciken gaggauta bayan ruftawar wani ɓangare na sabon ginin majalisar dokokin jihar
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya jajanta wa iyalan wanda ya rasu a iftila'in tare da cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin jinyar wadanda suka jikkata
  • An bai wa kamfanin ginin da masu kula da aikin wa'adin sa'o'i 24 su gabatar da cikakken rahoton musabbabin aukuwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta ba da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan ruftawar wani ɓangare na rumfar shiga sabon ginin Majalisar Dokokin Jihar Gombe da ake ginawa.

Lamarin, wanda ya faru a ranar Juma'a, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata ma'aikatan gini bakwai.

Gwamnatin Gombe ta dauki mataki da aka samu wani bangare na ginin majalisar jihar ya rufta kan ma'aikata
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya na jagorantar wani taro a gidan gwamnatin Gombe. Hoto: @OfficialGmsg
Source: Twitter

An fara bincikewar rushewar gini

Gwamnati ta fara bincike domin gano musabbabin ruftawar wani ɓangare na rumfar shiga sabon ginin Majalisar Dokokin jihar Gombe, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Qatar ta ware kwanakin makoki, ta ba da hutun aiki bayan mutuwar tsohon Sarki

A cikin wata sanarwa da sakataren dindindin na Ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Danladi Adamu, ya fitar, gwamnatin ta ce sashen da ya rufta wani ɓangare ne na rumfar shiga ginin da ake ci gaba da ginawa.

Sanarwar ta ce ma'aikata biyar daga cikin waɗanda suka jikkata na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Jihar Gombe, yayin da wasu biyu ke samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH), Gombe.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi martani

Gwamna Inuwa Yahaya ya jajanta wa iyalan mamacin tare da ba da umarnin ɗaukar nauyin jinyar dukkan ma'aikatan da suka jikkata.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutumin da ya rasu.

Ya kuma ba da umarnin cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin kula da lafiyar dukkan ma'aikatan da suka jikkata har sai sun warke.

Bugu da ƙari, gwamnan ya umurci Ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri tare da hukumomin gaggawa, na sa ido da kuma ƙwararrun injiniyoyi su fara bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

An dura kan kamfanin da ke ginin

Kamfanin ginin da masu kula da aikin sun samu wa'adin sa'o'i 24 su gabatar da rahoton abin da ya faru ga gwamnatin jihar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ginin Majalisar dokokin jihar Gombe ya rufta kan mutane ana tsakiyar aiki

A matsayin wani ɓangare na binciken, gwamnatin ta umarci kamfanin da ke gudanar da aikin da kuma masu kula da shi su gabatar da cikakken rahoton abin da ya faru cikin sa'o'i 24.

Haka kuma, an buƙace su su gabatar da rahoton binciken farko, sannan daga baya su miƙa cikakken rahoton fasaha da zai ƙunshi sakamakon bincike da shawarwarin da suka dace.

Gwamnatin jihar ta ce sakamakon binciken ne zai jagoranci matakan da za ta ɗauka, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da bin ƙa'idojin tsaro, inganci da ƙa'idodin aikin injiniya a dukkan ayyukan gine-ginen gwamnati.

Kwararren mai zanen gidaje ya yi martani a kai

Legit Hausa ta zanta da kwararren mai zanen gidaje, kuma Majikiran Gona, Architect Mohammed Abubakar Akko, dan jihar Gombe, wanda ya yi tsokaci kan rushewar wannan gini.

An ba gwamnatin Gombe shawara bayan gini ya rufta kan mutane
Taswirar jihar Gombe, inda ginin majalisa ya rubta kan ma'aikata. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mohammed Akko, ya bayyana cewa:

"A matsayi na na ƙwararren masani kan harkokin gine-gine, bai dace a yi gaggawar yanke hukunci kan musabbabin rushewar ginin ba kafin a kammala bincike.
"Ya kamata a gudanar da bincike mai zaman kansa, wanda zai kasance a bayyane ga kowa domin gano ainihin abin da ya haddasa matsalar da ta janyo rushewar sassan ginin.

Kara karanta wannan

Bene ya ruguzo a Kano, an samu asarar rai da raunata wasu mutane

"Ina kira ga gwamnatin jihar Gombe, Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje da sauran hukumomin da abin ya shafa su riƙa bai wa ƙwararrun 'yan asalin jihar damar taka muhimmiyar rawa a manyan ayyukan gwamnati.
"Ba lallai ne sai sun kasance 'yan kwangila ba, amma za a iya amfani da su a matsayin masu ba da shawara, masu sa ido kan ayyuka, masu bibiyar aiwatar da ayyuka da kuma masu tabbatar da ingancin gine-gine.
"Hakan zai ƙarfafa tsarin sa ido tare da rage yiwuwar amfani da kayan da ba su dace ba ko kuma aikata kura-kuran da kan haddasa rushewar gine-gine."

Bene ya ruguzo kan mutane a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu uku suka jikkata bayan wani bene mai hawa biyu da ake ginawa ya rushe a jihar Kano.

Benen ya rushe a kan titin Sultan da ke cikin birnin Kano a safiyar ranar Juma'a, 10 ga watan Yulin shekarar 2026

Jami'in hulɗa da jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com