Adamawa: Gwamna Ahmadu Fintiri ya rattaba hannu a kan sabuwar doka

Adamawa: Gwamna Ahmadu Fintiri ya rattaba hannu a kan sabuwar doka

- Gwamnatin Adamawa ta kawo dokar da ta halasta mata binciken gidajen Jama’a

- Ahmadu Umaru Fintiri ya kawo wannan doka domin dawo da kaya da aka sace

- Wasu tsageru sun fasa dakunan ajiya sun saci dukiyar 'yan kasuwa da gwamnati

Daily Trust ta ce gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya rattaba hannu a kan dokar da ta ba shi cikakken ikon bi gida-gida su yi bincike.

Gwamnatin Adamawa za ta bibiyi gidajen jama’a domin gano wadanda su ka wawuri dukiyar gwamnati da ta Bayin Allah daga dakunan adana.

A ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, 2020, gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bada wa’adin sa’a 12 domin jama’a su dawo da kayan da su ka sace.

KU KARANTA: An kai babban Jigon APC Tinubu gaban kotu, takardun shari’a sun babbake

Da wannan mataki da gwamnan ya dauka, wa’adin da ya bada ya cika a ranar Laraba da safe.

Sakataren yada labarai na gwamnan Adamawa, Humwashi Wonosikou, ya ce mai gidansa ya rattaba hannu kan doka mai iko mai lamba 2 ta 2020.

“Gwamnan ya yi la’akari da yadda jama’a su ke bin umarnin da aka bada a baya na cewa barayi su dawo da kayan da su ka fasa dakuna su ka sace.”

A dalilin haka, Humwashi Wonosikou ya ce: “Gwamna ya tsawaita wa’adin da ya bada da karin sa’a 12.”

KU KARANTA: An turo a kona mani gida, Jama'a su ka hana – Dino Melaye

Adamawa: Gwamna Ahmadu Fintiri ya rattaba hannu a kan sabuwar doka
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya rattaba hannu a sabuwar doka
Asali: UGC

Saboda haka za a fara binciken gida-gida ne da karfe 7:00 na safe a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, 2020.

Daily Trust ta ce jawabin da ya yi ya nuna cewa har yanzu dokar hana fita da aka sa ta na aiki.

Duk mai bayanin da zai ba gwamnati zai iya tuntubar: 08089671313, 08067592714.

A jihar Filato, an ji cewa tsagerun da su ka wawuri dukiyar Jama’a a lokacin zanga-zanga za su tafi kukurku. An shiga kotu da mutane 300 da aka kama sun wawuri kayan tallafi.

Laifuffukansu sun hada da sata, tada zaune tsaye, addabar Bayin Allah da sauransu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel