'Yan Najeriya 9 da za'a fafata dasu a zaben kasar Amurka

'Yan Najeriya 9 da za'a fafata dasu a zaben kasar Amurka

- A ranar Talata, uku ga watan Nuwamba, za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a kasar Amurka

- Amurkawa na da zabin kada kuri'a ga daya daga cikin 'yan takara guda biyu; Donald Trump da Sanata Joe Biden

- Trump ya na takara ne a karkashin inuwar jam'iyyar 'Republican' yayin da Biden ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar 'Democrat'

Mutum tara ne ƴan asalin Najeriya zasu fafata a zaɓen ƙasar Amurka mai zuwa a matakai daban-daban na tarayya,jiha da kuma ƙananan hukumomi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa baya ga zaɓen shugaban ƙasa da za'a gudana a ƙasar Amurka, akwai zaɓen gwamnoni a jihohi goma sha ɗaya da manyan birane gida biyu, da ƙarin wasu jihohin da kuma ƙananan hukumomi.

Zaɓen ƴan majalisu 435 da sanatoci 100 shima yana cikin jadawalin zaɓen da za'a fafata a cikinsa.

Ƴan Najeriya masu neman takara da za'a fafata dasu sun haɗar da; Oye Owolewa, Yomi Faparusi, Yinka Faleti, Paul Akinjo, Adewunmi Kuforiji, Esther Agbaje, April Ademiluyi, Ngozi Akubuike da Benjamin Osemenam.

KARANTA: kuɗin ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i

Mr Oye Owolewa yana neman wakilcin District of Columbia a ƙarƙashin jam'iyyar Democrat.

Idan har yaci zaɓen shine zai zamo ɗan Najeriya na farko da ya taɓa riƙe wannan mukamin a tarihin ƙasar Amurka.

A matakin tarayya Mr Yomi Faparusi na neman takarar Sanata mai wakiltar jihar Tennessee a ƙasar Amurka.

'Yan Najeriya 9 da za'a fafata dasu a zaben kasar Amurka
'Yan Najeriya 9 da za'a fafata dasu a zaben kasar Amurka @Punch
Asali: Twitter

Ba wannan ne karo na farko da Faparusi ya tsaya takara ba, sai dai duk lokutan baya da ya tsaya, har sau biyu, ya sha kaye; a shekarar 2014 da 2016.

Mr Yinka Faleti na neman takarar ofishin sakataren jiha a jam'iyyar Democrat a jihar Missouri.

Mr Paul Akinjo na neman wakiltar majalisar jihar Kalifoniya a ƙarƙashin jam'iyyar Democrat don ya wakilci District 12.

KARANTA: Sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan bindigar arewacin Najeriya a kan Ba-Amurke guda daya

Adewunmi Kuforiji na neman wakilcin District 34 a majalisar jihar Delaware.

Ms Esther Agbaje, na neman wakilcin majalisar wakilai a Minnesota a ƙarƙashin jam'iyyar Democratic farmer labor Party, jam'iyya mai haɗe da Democratic party ta Amurka.

A matakin masu takarar ƙaramar hukuma akwai April Ademiluyi, Ngozi Akubuike, da Benjamin Osemenam.

Ademiluyi na neman takarar Alƙalin kotun Seven Circuit a babbar kotun jihar Prince George dake Maryland.

Akuibuike a ɓangarenta itama yar takara ce mai zaman kanta a Minnesota 2nd District Court.

Osemenam na neman takara a Brooklyn Park City a jihar Minnesota don wakilcin gabashin yankin.

A karshen mako ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa an soke al-amurran yaƙin neman zaɓen Sanata Joe Biden ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka a inuwar jam'iyyar Democrat sakamakon barazana daga magoya bayan shugaba Donald Trump.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng