Brazil da Wasu Kasashe 10 da Suka Fi Zura Kwallaye a Tarihin Gasar Kofin Duniya

Brazil da Wasu Kasashe 10 da Suka Fi Zura Kwallaye a Tarihin Gasar Kofin Duniya

  • Brazil da Jamus sun ci gaba da zama ƙasashen da suka fi cin ƙwallaye a tarihin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA
  • Argentina da Faransa na ci gaba da matsowa gaba, yayin da suke cikin ƙasashen da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a 2026
  • A hannu daya kuma, Spain da Ingila na da damar ƙara yawan ƙwallayensu yayin da gasar cin Kofin Duniya ta 2026 ke dab da ƙarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da 10 a aikin jarida.

Gasar cin Kofin Duniya ta FIFA 2026 na ci gaba da samar da sababbin tarihi, yayin da manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa ke ci gaba da mamaye jerin ƙasashen da suka fi cin ƙwallaye a tarihin gasar.

Duk da ficewarsu da wuri daga gasar bana, Brazil da Jamus sun ci gaba da riƙe matsayinsu na farko da na biyu a jerin ƙasashen da suka fi zura ƙwallaye a tarihin Kofin Duniya.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za a kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

An jero kasashe 11 da suka fi cin kwallaye a gasar Kofin Duniya.
Hoton wani butuntumin Kofin Duniya da aka ajiye a lokacin bude gasar Kofin Duniya ta 2026 a Los Angeles, ranar 12 ga Yuni, 2026. Hoto: MB Media
Source: Getty Images

Kwallayen Brazil da Jamus a Kofin Duniya

Brazil da Jamus sun ci gaba da mamaye saman jerin ƙasashen da suka fi cin ƙwallaye duk da ficewarsu da wuri daga gasar ta 2026, a cewar rahoton TVC News.

Sababbin alkaluman FIFA da aka sabunta bayan wasannin ranar 10 ga Yulin 2026 sun nuna cewa Brazil mai kambun duniya sau biyar ce ta fi kowace ƙasa cin ƙwallaye a tarihin gasar.

Brazil ta zura ƙwallaye 247 a wasanni fr119, yayin da Jamus mai kambun duniya sau huɗu ke biye da ita da ƙwallaye 243 daga wasanni 116.

Ko da yake Brazil ta fita a zagayen 'yan 16, Jamus kuma ta yi bankwana tun a zagayen 'yan 32, tarihin da suka gina tsawon shekaru ya sa har yanzu suke kan gaba.

Kasashen da ke motsawa a cin kwallaye

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Argentina da Faransa na ci gaba da matsowa gaba yayin da Spain da Ingila ke da damar ƙara yawan ƙwallayensu a gasar bana

Kara karanta wannan

Mbappe da Dembele sun rusa burin Moroko, Faransa ta kai wasan kusa da na ƙarshe

Argentina mai riƙe da kambun duniya tana matsayi na uku da ƙwallaye 166, sai Faransa ta huɗu da 152, yayin da Italiya ke matsayi na biyar da kwallaye 128, duk da cewa ba ta samu tikitin shiga gasar 2026 ba.

Faransa, ƙarƙashin jagorancin Kylian Mbappe da Ousmane Dembele, ta kai wasan kusa da na ƙarshe inda za ta kara da Spain.

Haka kuma, Argentina ta Lionel Messi da Ingilar Harry Kane har yanzu suna cikin gasar, kuma suna da damar ƙara yawan ƙwallayensu a tarihin Kofin Duniya.

Messi na daga cikin 'yan wasan da suka kafa tarihi wa kasarsu a gasar Kofin Duniya 2026
Messi yana murna bayan ya ci wa Argentina kwallo a karawarsu da Egypt a gasar Kofin Duniya 2026. Hoto: Elsa via Getty Images
Source: Getty Images

Kasashen da suka fi cin kwallaye a Kofin Duniya

Jerin ƙasashe 10 da suka fi cin ƙwallaye a tarihin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA bayan sabunta alkaluma ranar 10 ga Yuli, 2026

Matsayi

Ƙasa

Yawan ƙwallaye

1

Brazil

247

2

Jamus

243

3

Argentina

166

4

Faransa

152

5

Italiya

128

6

Spain

119

7

Ingila

115

8

Netherlands

107

9

Uruguay

92

=10

Hungary

87

=10

Sweden

87

Faransa ta je zagayen Semi Fainal

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Faransa ta doke Moroko da ci 2-0, inda Mbappe da Dembele suka zura ƙwallaye suka kai Les Bleus wasan kusa da na ƙarshe.

Kara karanta wannan

An yi wa Amurka kaca kaca a kofin duniya duk da shiga da fitar Trump a boye

Mbappe ya ci ƙwallo a minti na 60 bayan ya kasa cin bugun fenariti a farkon wasan, wanda ya fara sanya farin ciki a zukatan 'yan Faransa.

Moroko ta kasa maimaita tarihin 2022 bayan ta sha kashi a hannun Faransa a gasar cin kofin duniya, inda a yanzu za ta koma gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com