Barna: Gwamna Fintiri ya sasauta dokar ta baci a jihar Adamawa

Barna: Gwamna Fintiri ya sasauta dokar ta baci a jihar Adamawa

- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Fintiri, ya sanar da dakatar da binciken gida-gida da aka fara a jihar Adamawa

- An fara binciken ne domin gano irin kayayyakin da mabarnatan matasa suka kwasa daga manyan shaguna ajiya mallakar gwamnati da 'yan kasuwa

- Kazalika, gwamnan ya sanar da sassauta dokar ta bacin da ya saka bayan batagarin matasa sun cigaba da tafka a jihar Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sassauta dokar ta baci ta tsawon sa'a 24 da ya saka bayan matasa sun cigaba da tafka barna a Yola.

A sanarwar da gwamnatin jihar Adamawa ta fitar, gwamna Fintiri ya ce sassauta dokar ta bacin za ta fara aiki ne daga ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoba.

Gwamna Fintiri ya saka dokar ta baci a jihar Adamawa bayan matasa sun fake da zanga-zangar ENDSARS domin cigaba da tafka barna a ma'adanan gwamnati da gine-gine mallakar hukuma.

A cewarsa, gwamati ta sassauta dokar ta bacin ne biyo bayan sake duban tsanaki a kan halin tsaro a fadin jihar.

"Gwamnati ta sassauta dokar ta baci ta tswon sa'a 24, jama'a za su iya domin gudanar da harkokinsu daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma daga ranar Juma'a, 30 ga wata Oktoba.

Barna: Gwamna Fintiri ya sasauta dokar ta baci a jihar Adamawa
Gwamna Fintiri
Asali: UGC

"Za mu sake sauya lokutan fita da dawowar mutane idan yanayi ya nun da bukatar hakan," a cewarsa.

Gwamnan ya bayyana cewa za a saka shingen binciken ababen hawa a hanyoyin shiga da fita daga jihar Adamawa.

"Za mu yi hakan ne domin tabbatar da cewa barayin da suka saci kayan gwamnati da na jama'a basu damar fita dasu daga jihar Adamawa ba.

A cewar gwamna Fintiri, ya zuwa yanzu an dawo da fiye da kaso 50% na kayayyakin da batagarin matasa suka sace daga shagunan ajiya mallakar gwamnati da 'yan kasuwa.

Kazalika, gwamna Fintiri ya sanar da gaggauta dakatar da binciken gida-gida da aka fara domin neman kayan da mabarbata suka wawashe a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel