Obi Ya Fada Tarkon Gwamnatin Tinubu, ana Barazanar Hukunta Shi
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bai wa Peter Obi kwana bakwai domin ya nemi afuwar ma'aikatan filin jirgin sama na Abuja
- Ya ce inciken da aka yi ta hanyar kyamarar CCTV ya nuna direban motar Obi ya bar mota a wuri da aka hana wucewa, bisa dokokin filin jirgi
- Keyamo ya ce an bar Obi ya tafi da motar ba tare da ya biya tarar N25,000 ba, kuma idan bai biya ba a cikin mako guda, FAAN za ta dauki mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya fitar da sanarwar cewa Peter Obi na NDC yana da kwana bakwai domin ya nemi afuwar ma'aikatan filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja.
Festus Keyamo ya bayyana cewa dole Peter Obi ya biya tarar N25,000 saboda laifin da ake zarginsa da shi a yayin da ya je filin jirgin.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a X, Keyamo ya ce hukumar ta gudanar da bincike, inda kyamarar CCTV ta filin jirgin ta nuna abin da ya faru, wanda ya saba da zancen da Obi ya yi na cewa an zalunce shi.
Me ya faru da Obi a filin jirgi?
A cewar ministan, lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Yulin 2026 lokacin da Obi ya isa filin jirgin saman Abuja kimanin karfe 8:28 na dare.
Ya ce bayan Obi ya sauka daga mota, direban ya ajiye motar a wuri da aka keɓe don saukar da masu tafiya kawai, amma ya bar ta ba tare da ya zauna a cikinta ba ya shiga cikin ginin filin.
Ministan ya ce direban ya dawo a takaitaccen lokaci sannan ya sake barin motar, wanda hakan ya sa ma'aikatan tsaron filin jirgin suka garkame tayun motar.
Bugu da kari, Keyamo ya jaddada cewa a lokacin da aka dauki matakin, ma'aikatan ba su san cewa motar ta Obi ba ce.
Bayan da direban ya gano an kulle motar, sai ya sanar da Obi, wanda a nasa bangaren ya yi magana da manajan filin jirgi ya nemi a sako motar.

Source: Facebook
Barazanar da aka yi wa Obi
Ministan ya yi ikirarin cewa barin mota a wurin da aka hana tafiya na tsawon kusan mintuna 30 haɗari ne mai girma ga tsaron filin jirgi, kuma yana saba wa ka'idojin tsaron jiragen sama na duniya baki ɗaya.
Keyamo ya kara da cewa Obi ya yi yunƙurin jan hankalin jama'a ta hanyar nuna kamar an zalece shi, duk da cewa an riga an warware lamarin kafin ya yi wannan magana a bainar jama'a.
Punch ta rahoto cewa ministan ya yi gargadi cewa idan Obi bai bayar da haluri ya biya tarar ba, zai umarci hukumar FAAN da ta ɗauki matakan da suka dace.
Maganar kashe Peter Obi
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya yi zargin cewa gwamnati na bibiyar rayuwarsa.
Peter Obi ya ce bisa abubuwan da suke faruwa da shi ta bayan fage, ba lallai rayuwarsa ta kai zaben 2027 ba, domin za a iya kashe shi.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya yi martani da cewa gwamnatin Bola Tinubu ba ta bibiyar rayuwarsa.
Asali: Legit.ng

