Malami Ya Fara Hango Yiwuwar Nasarar Sheikh Pantami a Zaben Gwamnan Gombe
- Kabir Danladi Lawanti ya yi nasa hasashen da yake nuna a halin yanzu tauraruwar Isa Ali Pantami tana haskawa
- Malamin jami’ar mai sharhi a kan al’amuran yau da gobe ya ce akwai abubuwan da za su iya taimakon PDP a Gombe
- Kasancewarsa malamin addini kuma akwai sabani a APC, Dr. Kabir Lawanti yana ganin Pantami zai iya kai labari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Dr. Kabir Danladi Lawanti malami ne a sashen koyar da aikin jarida a jami’ar ABU Zariya, ya tabo zancen siyasar jihar Gombe.
Malamin jami’ar ya tofa albarkacin bakinsa game da takarar da tsohon abokin aikinsu, Farfesa Isa Ali Pantami a zaben gwamnan Gombe.

Source: Facebook
Hasashen takarar Isa Pantami a jihar Gombe
A ranar Talata, malamin ya yi amfani da shafin Facebook, ya yi hasashen cewa babu mamaki Isa Ali Pantami ya iya zama gwamna a 2027.
Dr. Kabir Danladi Lawanti ya yi la’akari da wasu abubuwa da suka nuna babu mamaki jama’a su juya wa jam’iyyar APC baya a Gombe.
Zaɓen 2027 na ta ƙara matsowa. A Gombe na lura odds ɗin na favouring Dr. Isah Ali Pantami gaskiya saboda dalilai kamar haka:
- Kabir Danladi Lawanti PhD
Malamin jami’ar wanda shi kan shi ‘dan asalin jihar Gombe ne kuma wanda ya saba sharhi a kan al’umuran yau da gobe ya jero hujjojinsa.
Abubuwan da ke taimakon Isa Ali Pantami
Kabir Lawanti ya nuna Sheikh Isa Pantami yana samun karbuwa saboda kasancewarsa babban malamin addinin Musulunci a Najeriya.
Tsohon ‘dan jaridar ya kuma duba yadda rikicin cikin gidan jam’iyyar APC zai iya kawo wa gwamna Inuwa Yahaya cikas a zabe mai zuwa.
Hana Sanata Danjuma Goje takara a APC zai iya taba karfin jam’iyyar mai mulki ganin irin farin jinin tsohon gwamnan musamman a yankinsa.
Akwai rade-radin da ake yi cewa za a bar wa PDP wasu jam’iyyu a zaben 2027. Jam’iyyar tana fama da rikicin cikin gida tun kafin zaben 2023.
Daga cikin abubuwan da aka ce suna jawo wa Pantami farin jini a kan Jamilu Gwamna shi ne ana ganin ya shi ya san makamar aiki sosai.

Source: Facebook
Kabir Danladi Lawanti ya rubuta:
Malam na da matuƙar goyon baya saboda matsayin shi na masanin addini. Talakawa musulmi suna matuƙar son shi.
Mutanen Gombe suna matuƙar jin haushin Inuwa Yahaya saboda irin yadda ya gudanar da jihar a cikin shekara takwas da yayi yana mulki. Fushin Inuwa zai iya shafar Jamilu.
Har yanzu Jamilu na jan ƙafa wajen reaching out to ƴan takara da aka kwarfe a zaɓen fidda gwani. So hushin wasu zai koma kan Jamilu.
Wasu na cewa Jamilu ya jima yana cin amanarsu a siyasa. Saboda haka za su rama yanzu.
Goje factor shima na nan. Wasu jira su ke su huce haushin su.
Gombe has been a PDP state for 16 years. Ko tana cikin jihohi da aka ce za'a barwa Wike ya samu gwamna? Ita ma wannan maganar akwai ta.
Pantami na da capacity.
A karshen rubutun na shi, ya ce wannan ra'ayinsa ne kawai la’akari da bayanan da yake samu daga mutane kuma nan gaba abubuwa za su fito fili da kyau.
Isa Pantami ya ziyarci Sule Lamido
Wannan rahoton ya yi bayani kan ziyarar da tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, tare da wasu 'yan takarar gwamna na PDP, suka kai zuwa Jigawa.
'Yan siyasar sun yi zama da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, a gidansa da ke garin Bamaina a kokarin ganin sun yi nasara a zaben shekara mai zuwa.
Sheikh Pantami ya nuna tsananin girmamawa ga Sule Lamido, inda ya bayyana shi a matsayin "uba" da kuma jagora mai kishin talakawa da ya gaji Aminu Kano.
Asali: Legit.ng



