2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi

- Yankin kudu maso gabas ta kafe kan samar da shugaban kasa na gaba a 2023

- A halin yanzu, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bi sahun wannan kira

- Umahi ya bayyana cewa domin samar da zaman lafiya da hadin kai, ya kamata magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito daga yankin

David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya shiga sahun masu ganin ya dace Shugaban kasa na gaba ya fito daga yankin arewa maso gabas.

Batun wanda zai karbi shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 na ta daukar dumi inda kungiyoyi da mutane ke ta muhawara kan yankin da ya kamata a mikawa shugabancin.

Da yake magana a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, Umahi, wanda ya kasance Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, ya bayyana cewa domin wanzar da adalci da kuma kare amincin kasa, ya kamata Shugaban kasa na gaba ya fito daga yankinsu.

KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe: Mazauna Legas sun roƙi ƴan sanda su koma bakin aiki

2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi
2023: Kudu maso gabas ne ya kamata ya samar da magajin Buhari – Gwamna Umahi Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Twitter

Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa wannan shine kiran da matasan yankin ke yi, jaridar Punch ta ruwaito.

Umahi ya kuma yaba ma jagororin zanga-zangar EndSARS kan ajiye komai a gefe tare da kawo karshen gangamin da suka yi a yankin kudu maso gabashin kasar.

Ya kuma yi Alla-wadai da harbe-harben Lekki sanan ya bayyana cewa gwamnonin kudu maso gabas za su ci gaba da kira ga “bincike domin hukunta masu laifin.”

Gwamnan ya yi alkawarin daukar bukatun masu zanga-zangar zuwa gaban Shugaban kasa da kuma tabbatar da ganin cewa komai ya koma daidai.

KU KARANTA KUMA: Muƙarraban gwamnati ne suka hamdame tallafin COVID-19 - Gwamna Yahaya Bello

“Ina ganin ya kamata a bari yankin kudu maso gabas ta samar da Shugaban kasar. Ina da tabbacin cewa abunda matasa ke so kenan.

“Mun yi tattaunawa masu amfani da matasan. Sun bukaci mu tattauna da Shugaban kasar kan bukatunsu,” ya ce.

A wani labarin, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Ebonyi ta bukaci jam’iyyar da ta mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu maso gabas.

Shugaban PDP a jihar, Onyekachi Nwebonyi, ya yi wannan rokon a yayinda yake jawabi ga manema labarai a Abakaliki a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel