Alpha Beta: Lauya ya ce zanga-zangar #EndSARS ta ci takardun kara a kotu

Alpha Beta: Lauya ya ce zanga-zangar #EndSARS ta ci takardun kara a kotu

- An samu matsala a karar da aka kai kamfanin Alpha Beta Consulting

- Lauya ya ce takardun shari’ar da su ka shigar a kotu sun kone kwanaki

- Hakan ya faru ne saboda an kona kotun Igbosere a wajen zanga-zanga

Jarridar Punch ta ce shari’ar da ake nema ayi da jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da kamfanin Alpha Beta Consulting ya samu tasgaro.

Lauyan da ya tsaya a madadin Dapo Apara a kotu, Tade Ipadeola, ya ce takardun karar da aka shigar sun kone a sanadiyyar zanga-zangar #EndSARS.

An kona wurare da-dama a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar #EndSARS, daga cikin inda aka kona har da babban kotun Legas da ke Igbosere.

KU KARANTA: Lauya ya bukaci Buhari da Gwamnatin Legas su biya diyyar N10bn

A wannan kotu na Igbosere ne aka shigar da karar Bola Tinubu. Lauyan da ya dumfari Alkali ya ce komai ya kone a kotun har da duk takardunsu.

“Komai ya kone a babban kotun Igbosere, daga ciki har da takardun da mu ka ba kotu na shari’armu.” Tade Ipadeola ya fada wa Punch jiya.

Lauyan ya cigaba da cewa: “Komai ya kone kurmus, ya zama toka. Saboda haka sai mun sake shigar da kara, an kuma maida takardun zuwa Ikeja.”

“Watakila dole mu shigar da sabuwar kara a babban kotun Ikeja, amma yanzu ba a ba mu umarnin yin hakan ba tukuna.” Inji Lauyan na Dapo Apara.

KU KARANTA: Gololo ya na so a goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2023

Alpha Beta: Lauya ya ce zanga-zangar #EndSARS ta ci takardun kara a kotu
Bola Tinubu Hoto: nationalmonitor.com.ng
Asali: UGC

Tsohon shugaban kamfanin Alpha Beta, Dapo Apara ya na karar babban ‘dan siyasar kasar, ya ce Bola Tinubu ya na karbar 10% na harajin da aka karba.

Ipadeola ya nemi kotu ta ba Bola Tinubu da Akin Doherty umarnin su bayyana a gaban Alkali.

A wannan zanga-zanga, Tinubu ya yi asara, wasu miyagu sun auka wa kamfanoninsa na jaridar The Nation da gidan talabijin na TVC, sun yi barna.

Tsohon Gwamnan jihar Legas ya ce bai da burin ganin an zubar da jinin masu zanga-zanga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel