Yaƙin Amurka da Kasar Musulunci Ta Iran Ya Zama 'Alheri' ga Attajirin Najeriya, Dangote
- Wani rahoto da aka fitar yau Juma'a, 10 ga watan Yulin 2027 ya nuna alherin da matatar Dangote ta samu sakamakon yakin Amurka da Iran
- Rahoton ya ce matatar hamshaƙin ɗan kasuwar ta amfana sosai saboda man da take tacewa ba ya bi ta mashigin Hormuz
- Matatar Dangote na ci gaba da fitar da kayayyakin ta kamar fetur, dizal da man jirgin sama zuwa kasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, na daga cikin manyan wadanda suka amfana da rikicin da ya barke tsakanin Amurka da Iran.
Wani rahoton bincike da aka fitar ya nuna cewa matatar Dangote ta samu alheri a yakin da ya gudana tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Rahoton, wanda jaridar Wall Street Journal (WSJ) ta wallafa yau Juma'a, ya nuna cewa, Dangote na ci gaba da girbar amfanin matatar man fetur ta Dala biliyan 20 da ya gina.
Matatar Dangote ta ci gajiyar rikicin Iran
A cewar WSJ, matatar ta kai cikakken karfin aiki tun watan Fabrairun wannan shekara, lamarin da ya ba ta damar samar da fetur, dizal da man jiragen sama ba tare da dogaro da mashigin Hormuz ba.
Rahoton ya ce karuwar bukatar wadannan kayayyakin ta kara wa Dangote dukiyarsa da kusan Dala biliyan 4.86 tun farkon shekarar nan, inda darajar dukiyarsa ta kai kusan Dala biliyan 34.8.
Hakan ya sanya shi cikin jerin mutane mafiya arziki na 65 a duniya, kamar yadda Bloomberg Billionaires Index ta nuna.
Matatar na shirin shiga kasuwar hannun jari
Mataimakin shugaban masana'antun Dangote, Devakumar Edwin, ya shaida wa WSJ cewa kamfanin na shirin sanya matatar fetur a Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX) kafin karshen shekarar nan.
Ya ce ana sa ran darajar matatar za ta kai akalla Dala biliyan 50, sannan kamfanin na duba yiwuwar sake shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York.
Bukatar kayayyakin matatar ta karu
Edwin ya bayyana cewa bukatar kayayyakin matatar Dangote ta karu sosai a kasashen yankin Afirka da ke kudancin Sahara, yayin da fitar da man jiragen sama zuwa Turai ma ta karu.
Ya kuma ce kamfanin na shirin fadada matatar zuwa iya tace ganga miliyan 1.4 a rana nan da shekarar 2028, aikin da ake sa ran zai lakume kusan Dala biliyan 13.

Source: Getty Images
Dangote zai gina sabuwar matata a Kenya
Baya ga haka, Edwin ya bayyana cewa Dangote na shirin gina wata sabuwar matatar mai a yankin Lamu da ke gabar tekun Kenya.
Ya ce aikin, wanda ya hada da gina tashar ruwa, zai dauki kusan shekara uku ana yi, tare da kashe kusan Dala biliyan 15.
A cewarsa, kamfanin ya riga ya zabi wurin da za a gina matatar kuma yana shirin fara aikin zane da tsarinta.
Matatar Dangote ta fara jigilar fetur kyauta
A wanai rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta fara jigilar fetur kyauta zuwa jihohi shida da Abuja ga masu sayen lita 250,000 ko fiye ba tare da karin kudin sufuri ba.
Wannan na zuwa ne yayin da matatar Dangote ta ci gaba da sayar da fetur a farashin Naira 1,075 kan kowace lita ga abokan huldarta.
Baya ga kai fetur kyauta, matatar ta ce masu sayen da suka cancanta.za su samu damar biyan kudin mai cikin kwanaki 10 bayan an kai musu kaya.
Asali: Legit.ng


