Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani a kan tsine mata a Masallatai

Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani a kan tsine mata a Masallatai

- Zangar-zangar lumana domin nuna kyamar rundunar 'yan sanda ta SARS ta rikide zuwa kazamin rikici a sassan Najeriya

- 'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, na daga cikin jagororin matasan da suka assasa tare da jagorantar zangar-zangar ENDSARS

- Sai dai, Aisha ta sha suka da caccaka daga wasu shugabannin siyasa, musammam ma su rike da mukamai, da kuma wasu malamai

'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda 'ta yi uwa, ta yi makarbiya' a zanga-zangar ENDSARS.

Aisha, wacce sunanta ya kara karada gari saboda zanga-zangar ENDSARS, ta ce ko kadan hakan bai taba damunta ba.

"Na ji cewa na sha tsinuwa a Masallatai, mutane suna zama domin kawai su tsinemin bayan sun idar da Sallah.

KARANTA: Harsashin roba ba ya kisa - SU Kukasheka ya yi karin bayani a kan zargin sojoji da kisan farar hula a Lekki

"Tambayata wurinsu guda daya ce; sau nawa suka yi min irin wannan tsinuwar a lokacin da nake caccakar tsohon shugaban kasa Jonathan! Dukkanmu tsinannu a Najeriya," kamar yadda Aisha ta rubuta, tare da hadawa da alamar shekewa da dariya, a shafinta na tuwita.

'Yar gwagwarmayar na daga cikin wadanda suka assasa tare da jagorantar matasan da suka fito domin gudanar da zanga-zangar ENDSARS.

Sai dai, zanga-zangar ENDSARS ba ta samu wata karbuwa ba a jihohin arewa, musamman jihohin yankin arewa maso yamma, da Aisha ta fito.

Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani a kan tsine mata a Masallatai
Aisha Yesufu yayin wata tattaunawa da wakilin Legit.ng
Asali: UGC

Zakewarta yayin zanga-zangar ya jawo mata shan suka da caccaka a wurin shugabannin siyasa, musammam masu rike da mukamai, da wasu malaman addini.

KARANTA: Idan Najeriya ta tarwatse a nan gaba, kiyayya ce ta tarwatsa ta - Femi Adesina

Zanga-zangar lumana ta neman a rushe rundunar 'yan sanda ta SARS ta rikide zuwa rikici da tarzoma a jihohi da dama.

Ganin irin tarzomar da zanga-zangar ta haifar ne yasa Ƙungiyar tuntuba da cigaban Arewa (ACF) ta yi gargaɗin cewa ya kamata shugabannin Najeriya su sani za a iya rasa zaman lafiya a kasa idan har suka cigaba da yin burus da matasa da kuma buƙatunsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel