Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni

Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni

- Gwamna Mai Mala Buni ya ce jam’iyyar APC bata riga ta yanke hukunci a kan yankin da za ta mika wa Shugaban kasarta ba a 2023

- Gwamnan na jihar Yobe ya kuma jaddada cewa ba a yanke hukunci kan daga inda sabon ciyaman na jam’iyyar zai fto ba

- A cewar Buni wanda ya kasance Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar mai mulki ta kasa, APC na kara gina kanta tare da sasanta fusatattun mambobinta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa ba ta yanke shawara kan yankin da za ta mika wa tikitin Shugaban kasa ba a 2023.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ta kasa, Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe, ya bayyana hakan a lokacin wata hira da jaridar Saturday Sun.

Legit.ng ta fahimci cewa tattaunawa kan wanda zai karbi shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 na kara daukar dumi.

Kungiyoyida mutane na ta sharhi kan inda ya kamata a mika kujerar shugabancin.

Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni
Shugabancin 2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba, Buni Hoto: @dailysunsa
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu

Manyan yan siyasa da suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagas Bola Tinubu, Gwamna Ahmad El-Rufai na Kaduna, Sanata Orji Uzor Kalu, da sauransu sun samu goyon baya domin karbar mulki daga hannun Buhari.

Hukumar zabe ta asa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewar za a yi zaben Shugaban kasa na gaba a ranar 28 ga watan Fabrairun 2023.

Yayinda ake ta tambaya kan inda APC za ta mika tikitin Shugaban kasarta bayan wa’adin Buhari/Arewa, Gwamna Buni ya ce jam’iyyar mai mulki na sake gina kanta tare da sasanta fusatattun mambobinta.

Ya bayyana cewa kwanan ne jam’iyyar ta tsallake rijiya da baya sakamakon rikicin shugabanci wanda ya yi sanadiyar tunkude shugabancin Adams Oshiomhole.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Sudais ya yi Allah-wadai da masu yin batanci ga Annabi

“Ba za mu iya cewa ga inda ciyaman ko Shugaban kasa na jam’iyyar zai fito ba. Ba za mu iya tsallake gada ba har sai mun kai wajen.

“A halin da ake ciki, kwamitin na aikin sake gina jam’iyyar ne ta yadda za ta iya jure duk wani abu a wannan lokaci da kuma ci gaba da kasance jam’iyya mai mulki a Najeriya."

A gefe guda, Kungiyar Nasiriyya a jihohi 21 sun bayyana aniyarsu ta janyo gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tsaya takarar shugaban kasa a babben Zaben 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel