Akpabio Ya Yi Hasashen Abin da 'Yan Adawa Za Su Ce idan Tinubu Ya Ci Zaben 2027

Akpabio Ya Yi Hasashen Abin da 'Yan Adawa Za Su Ce idan Tinubu Ya Ci Zaben 2027

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa jam'iyyun adawa sun shirya abin da za su fada bayan an ayyana shugaban kasa a 2027
  • Akpabio ya bayyana hakan ne bayan yakininsa na cewa shugaba mai ci Bola Ahmed Tinubu ne zai koma kujerarsa bayan an kammala kada kuri'a a zaben
  • Ya bayyana haka ne a wta tattaunawa da ya yi da 'yan kungiyar City Boy da suka dauko tallata Tinubu a fadin Najeriya gabanin siyasar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce yana hasashen jam'iyyun adawa za su rika ikirarin cewa an tafka magudin zabe idan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake samun nasara.

Kara karanta wannan

"Sauran jam'iyyu suna bacci," Akpabio ya fadi yadda Tinubu zai lashe zaben 2027

Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar City Boy da ke tallata Tinubu ta kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.

Akpabio ya ce Tinubu zai yi nasara a 2027
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Akpabio ya yabawa kungiyar kan yadda take fadada ayyukanta a fadin kasar nan domin hada kan magoya bayan Tinubu da kuma karfafa goyon baya ga sake tsayawarsa takara a zaben da ke tafe.

Akpabio ya fada wa yan adawa magana

A ruwayar jaridar Vanguard, Akpabio ya ce kungiyar na kara samun karbuwa a sassa daban-daban na Najeriya, lamarin da ya ce sauran jam'iyyun siyasa sun fara fahimtar tasirinta.

Akpabio ya bayyana cewa da an samu kungiyar kafin zaben 2023, da kuri'u da dama da aka ce ba a kirga ba a wasu rumfunan zabe za su samu kariya ta hanyar kasancewar wakilan jam'iyyar a wuraren zaben.

Shugaban majalisar dattawan ya bukaci 'yan kungiyar su kara himma wajen wayar da kan masu kada kuri'a da kuma karfafa masu gwiwar shiga harkokin zabe kafin babban zaben 2027.

Ya ce yayin da kungiyar ke zagayawa sassan kasar nan tana fadakar da jama'a, wasu jam'iyyun siyasa ba sa gudanar da irin wannan aiki, amma daga baya za su fara zargin magudi idan aka sanar da sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Atiku ba zai yi nasara ba a zaben shugaban kasa na 2027'

Akapbio ya yabi masoyan Tinubu

Akpabio ya kuma bayyana cewa kungiyar ta samar wa matasan Najeriya dama ta koyon dabarun jagoranci, tattara magoya baya da gudanar da yakin neman zabe domin amfaninsu a nan gaba.

Akpabio ya ce majalisa za ta goyi bayan masoya Tinubu
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hpoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Ya ce majalisar dattawa tana goyon bayan matasan da suka zabi bin tafarkin zaman lafiya, tare da gujewa ta'addanci, daba da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Hakazalika, ya gargadi matasan da kada su bari munanan halaye su lalata makomarsu, yana mai cewa Najeriya na bukatar matasa masu nagarta da za su taka rawar gani wajen gina kasa.

Akpabio, wanda shi ne babban majiɓincin kungiyar City Boy, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da samun goyon bayan majalisar dattawa muddin suna tafiya a kan turbar da ta dace.

Tinubu ya ba ICPC umarni

A baya, kun samu labarin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta ICPC umarnin bincike kan wata cibiyar gwamnati ta bogi da ake kira PFIPC da ake ta cece-kuce a kanta.

Kara karanta wannan

Yadda haduwa da Peter Obi zai jawo wa Kwankwaso asarar kuri'a a 2027

Wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya kira kansa a matsayin shugaban hukumar, inda ya ce shugaban kasa ne ya nada shi lamarin da fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin karya tsagwaronta.

Shugaban ksa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa hukumar ICPC kwanaki 30 domin kammala bincike tare da gabatar da cikakken rahoto a gare shi a kan wannan al'amari da ya ja hankali a ciki da wajen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng