An sace $2m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka

An sace $2m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka

- A cikin watan Nuwamba za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a kasar Amurka

- Amurkawa na da zabin kada kuri'a ga daya daga cikin 'yan takara guda biyu; Donald Trump da Sanata Joe Biden

- Trump ya na takara ne a karkashin inuwar jam'iyyar 'Republican' yayin da Biden ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar 'Democrat'

Jami'an jam'iyyar 'Republican' a jihar Wisconsin sun ce barayin yanar gizo sun sace Dala miliyan biyu ($2m) daga asusun da ake tara kudin yakin neman sake zaben Donald Trump a Amurka.

A ranar uku ga watan Nuwamba ne Amurkawa zasu kada kuri'unsu ga daya daga cikin 'yan takara biyu; Donald Trump, da Sanata Joe Biden, da ke neman kujerar shugaban kasa.

Andrew Hitt, shugaban jam'iyyar 'Republican' ta shugaba Trump a jihar Wisconsin, ya ce sun ankara cewa an sace kudin ne a ranar 22 ga watan Oktoba.

KARANTA: Zamfara: An yi batakashi tsakanin sojoji da 'yan bindiga, ba a san adadin wadanda suka mutu ba

Sai dai, Hitt ya bayyana cewa tuni 'yan sandan tarayya (FBI) sun fara gudanar da bincike a kan lamarin.

Jihar Wisconsin na da matukar tasiri a zaben 2020, saboda, da kyar shugaba Trump ya samu nasara da banbancin kuri'u 23,000 a zaben shekarar 2016.

An sace $2m daga kudin yakin neman zaben Trump a Amurka
Donald Trump @independent
Asali: Twitter

"Tabbas bacewar kudin za ta iya shafar nasarar jam'iyyar Republican a Wisconsin," a cewar Hitt, yayin da yake magana a kan bukatar kudi domin su kara matsawa da yakin neman zabe a irin wannan lakaci.

Kamfanin dillacin labarai na 'Associated Press' ya rawito Hitt na cewa barayin sun yi amfani da kwarewa wajen yaudarar masoya Trump ta hanyar basu takardar shaidar bawa Trump tallafi ta bogi.

KARANTA: Harsashin roba sojoji suka yi amfani da shi a kan masu zanga-zanga - SU Kukasheka

Barayin sun sauya wasu bayanai a jikin takardar neman tura tallafi zuwa asusun tarawa Trump kudin yakin neman zabe a jihar Wisconsin, a cewaer Hitt.

Hitt ya kara da cewa barayin har huluna da takardun yakin neman zaben Trump suke aikawa masoya Trump a matsayin tukuicin tallafin da suka bayar.

A ranar Juma'a ne Sanata Joe Biden, dan takarar 'Democrat' zai ziyarci jihar Wisconsin. Kazalika, shi ma shugaba Trump zai sake ziyarar jihar Wisconsin, a karo na uku, a ranar Juma'a.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito shugaba Trump yana cewa zai iya yin hijira ya bar kasar Amurka idan har bai samu damar sake lashe zabe mai zuwa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel