‘Saboda Ni Dan Arewa ne’: Dan Super Eagles kan Nuna Masa Wariya a Enugu Rangers
- Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Moses Simon, ya zargi Enugu Rangers International da ƙin ba shi kwantiragi a baya saboda wariya
- Rangers ta musanta zargin Simon, tana mai cewa dukkan ɗaukar 'yan wasa a kulob ɗin ana yin su ne bisa ƙwarewa, hali da jajircewa
- Kulob ɗin ya jaddada cewa tsawon shekaru yana ba 'yan wasa daga sassa daban-daban na Najeriya dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ɗan wasan Super Eagles, Moses Simon, ya bayyana yadda ya fuskanci wariya a Kudancin Najeriya.
Simon ya yi zargin cewa kulob ɗin Rangers International ya taɓa hana shi kwantiragin ƙwararrun 'yan wasa shekaru da suka wuce saboda bambancin ƙabila.

Source: Getty Images
A wata hira da Urban Dwell Sports, Simon ya ce ya shafe watanni uku yana gwaji tare da Rangers, har ma ya jagoranci tawagar gwajin.
Ya ce duk da hakan, kulob ɗin ya ɗauki wani ɗan wasa da ya yi atisaye na mako guda kacal, yayin da shi aka ƙi ba shi kwantiragi saboda ya fito daga Arewa.
Simon wanda ya tashi a Kaduna kuma dan asalin jihar Benue ya ce wannan shi ne karo na farko da yake bayyana labarin, yana mai cewa ba rashin ƙwarewa ya sa aka ƙi ɗaukarsa ba.
Ya ce ya yi imanin cewa asalinsa daga Arewacin Najeriya ne ya sa aka nuna masa wariya, yana mai cewa an gaya masa hakan ne a lokacin.

Source: Getty Images
Martanin Enugu Rangers kan zargin Simon
Babban Manaja kuma Shugaban Rangers, Amobi Ezeaku, ya fitar da wata sanarwa wanda ya sanya wa hannu aka kuma wallafa a Facebook.
kulob ɗin da ke Enugu ya musanta wannan zargi, yana mai cewa dukkan matakan ɗaukar 'yan wasa a cikinsa suna dogara ne da ƙwarewa, ba ƙabila ko asali ba.
Enugu Rangers ta ce bata taɓa nuna wariya bisa ƙabila, addini ko yankin da mutum ya fito ba.
Rangers ta ce duk da kasancewarta kulob daga Enugu da Kudu maso Gabas, fiye da shekaru hamsin tana karɓar 'yan wasa, masu horarwa da jami'ai daga sassa daban-daban na Najeriya da nahiyar Afirka.
Kulob ɗin ya bayyana cewa tsarin zaɓen 'yan wasa yana dogara ne da bajinta, hali, ladabi da jajircewa, ba wai ƙabila ko asalin mutum ba.
Rangers ta ƙara da cewa dubban 'yan wasa sun ratsa kulob ɗin tsawon shekaru, inda wasu suka samu kwantiragi, wasu kuma ba su samu ba saboda dalilan fasaha da gudanarwa.
Kulob ɗin ya ce ba daidai ba ne a bayyana shi a matsayin mai nuna wariya, domin ƙungiyoyin maza, mata da matasa na ci gaba da maraba da hazaka daga ko'ina cikin Najeriya.
A ƙarshe, Rangers ta ce za ta ci gaba da bai wa kowane hazikin ɗan wasa dama ba tare da la'akari da ƙabila, addini ko yankin da ya fito ba, tana mai jaddada cewa bajinta ce ke ba da dama, ba ƙabila ba.
Kofin Duniya: Wike ya tura sako ga Super Eagles
An ji cewa ana ci gaba da buga wasanni a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 a kasashen Amurka, Canada da Mexico.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya nuna rashin jin dadinsa saboda rashin kasancewar Najeriya a gasar.
Wike ya bayyana cewa kasashen da ba a sansu ba ma sun samu gurbi a gasar amma Najeriya kuwa ta gaza zuwa.
Asali: Legit.ng

