Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sun yi wa tawagar Joe Biden barazana da makamai

Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sun yi wa tawagar Joe Biden barazana da makamai

- A cikin watan Nuwamba za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a kasar Amurka

- Amurkawa na da zabin kada kuri'a ga daya daga cikin 'yan takara guda biyu; Donald Trump da Sanata Joe Biden

- Trump ya na takara ne a karkashin inuwar jam'iyyar 'Republican' yayin da Biden ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar 'Democrat'

An soke al-amurran yaƙin neman zaɓen Sanata Joe Biden ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka a inuwar jam'iyyar Democrat sakamakon barazana daga magoya bayan shugaba Donald Trump.

Ƴan jam'iyyar Democrat sun ce an soke gangamin yaƙin neman zaɓen ne wanda aka shirya yinsa ranar juma'a a Pflugerville, wani gari a Texas, saboda dalilai na tsaro da shawarwari makamantan hakan.

Acewarsu, motar yaƙin neman zaɓen Biden/Harris ta tsaya cak a kan hanya sakamakon tsinke da gungun magoya bayan Trump suka yi mata.

KARANTA: Sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan bindigar arewacin Najeriya a kan Ba-Amurke guda daya

Ƴan jam'iyyar Democrat sun yi zargin magoya bayan Trump sun ci gaba da bin bayan motar a yunƙurinsu na ganin sun hana al-amuran yaƙin neman zaɓen Biden gudanawa a manyan jihohin da za'a fafata ranar zabe.

Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sun yi wa tawagar Joe Biden barazana da makamai
Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sun yi wa tawagar Joe Biden barazana da makamai
Asali: UGC

Rafael Anchìa, guda daga cikin ƴan majalisar wakilan Texas, ya ce wasu daga cikin ƴan tawayen na ɗauke da makamai.

"An gano magoya bayan Trump ɗauke da makamai suna cin mutuncin mototoci masu bamu gudunmawar yaƙin neman zaɓenmu.

KARANTA: Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

"Sun tsare tituna na tsawon mintuna 30 zuwa 40 don ganin sun hana abubuwa tafiya yadda ya kamata," a cewar Anchia.

Anchía yayi zargin Eric, ɗa ga Trump, shine ya haddasa tarzomar.

Shi ma Sheryl Cole, ɗan jam'iyyar Democrat mai neman mulki a karo na biyu, ya ce; "haƙiƙa ƴan tarzoma da ke goyon bayan Trump sun wuce makaɗi da rawa.

"Ina tausayawa masu son ganin sun hana mu sakat."

Texas na da guraben zaɓe guda 38 wanda hakan ya bata damar kasancewa ta biyu a yawan masu kada a ƙasar Amurka.

A ranar Juma'a ne Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa shugaban jam'iyyar 'Republican' a jihar Wisconsin ya ce barayin yanar gizo sun sace Dala miliyan biyu ($2m) daga asusun da ake tara kudin yakin neman sake zaben Donald Trump a Amurka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel