‘Yan iskan Gari sun auka wa Sakatariyar APC a Jihar Delta, sun yi gaba da kaya

‘Yan iskan Gari sun auka wa Sakatariyar APC a Jihar Delta, sun yi gaba da kaya

- ‘Yan iskan-gari sun kai hari a wata sakatariyar jam’iyyar APC a Jihar Delta

- Jam’iyyar APC ta tabbatar da wannan farmaki da aka kai mata a makon jiya

- An yi gaba da wasu kayan jam’iyya, sannan an nemi a rusa ginin hedikwatar

Wasu miyagu da su ka shiga cikin rigar zanga-zangar lumunar #EndSARS sun kai wa hedikwatar jam’iyyar APC hari a jihar Delta.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, ta ce wannan lamarin ya auku ne a cikin karamar hukumar Udu da ke Delta.

Bata-garin sun yi awon-gaba da wasu kaya da su ka samu a hedikwatar jam’iyyar, bayan haka sun yi fata-fata da kayan da su ka samu.

KU KARANTA: Janar Buratai ya gana da manyan Jami'an soji

Bugu da kari, wadannan ja’irai sun yi kokarin ruguza ginin ofishin jam’iyyar kafin wasu matasa su kawo dauki, su hana ayi hakan.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Mista Sylvester Imonina, ya tabbatar wa manema labarai da wannan hari da aka kai.

Imonina ya ce wasu miyagu ne da su ka yi basaja da ‘yan zanga-zanga su ka yi wannan aiki.

Da ya ke magana, Imonina ya ce babu dalilin da za a kai hari a ofishin jam’iyyar da ba ta taba rike mulki a jihar Delta tun 1999 ba.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Shugaban karamar hukuma a Oyo

‘Yan iskan Gari sun auka wa Sakatariyar APC a Jihar Delta, sun yi gaba da kaya
Masu zanga-zangar EndSARS Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Delta APC ta yi kira ga jami’an tsaro su kara kokarin da su ke yi na kare rayuka da dukiyar mutanen jihar, musamman ‘ya ‘yanta.

Mai magana da yawun APC ya ba masu wannan mugun nufi shawarar su tuba kafin ayi ram da su.

Ana bukatar N1tr wajen sake gina Jihar Legas. Femi Gbajabiamilla ya ce za a bukaci wannan kudi domin maida barnar da #EndSARS ta yi

Shugaban Majalisar ya kuma nuna Majalisa za ta tsayawa iyalan wadanda aka kashe a rikicin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel