Yadda Sojoji Suka Kutsa Dajin Oyo, Suka Gwabza da 'Yan Bindiga yayin Ceto Dalibai
- Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun ceto dalibai da malamai 44 da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo tun ranar 15 ga Mayu 2026
- Ayyukan ceto daliban sun dauki sama da wata guda, kuma an kama wasu daga cikin shugabannin 'yan ta'addan a jihohi da dama
- A yanzu haka, wadanda aka ceto na karbar kulawar likitoci a asibitin da ba a bayyana sunansa ba kafin a mayar da su ga gwamnatin jihar Oyo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ibadan - Sojin Najeriya sun ba da rahoton cewa an ceto dalibai da malamai 44 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Oriire a jihar Oyo, bayan da aka gudanar da wani babban aiki na tsaro tare da haɗin gwiwar hukumomi da dama.
An samu nasara a aikin ne a ranar 10 ga Yulin 2026, inda Manjo Janar CR Nnebeife, wato Babban Hafsan Rundunar Soja ta 2 da ke Ibadan, ya jagoranci dakaru.

Source: Facebook
Rundunar sojin Najeriya ta wallafa a Facebook cewa an dauki wadanda aka yi garkuwa da su tun ranar 15 ga Mayu 2026, wato sun kwashe sama da wata ɗaya a hannun 'yan ta'adda.
Yadda aka ceto daliban Oyo
Ayyukan sun tattaro hukumomi da yawa, ciki har da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (ONSA), cibiyar yaki da ta'adda ta kasa (NCTC), sojojin sama, sojojin ruwa, 'yan sanda, DSS, NIA, NSCDC, mafarauta da ƙungiyar Amotekun.
Jami'an tsaro sun mai da hankali kan gano wuraren da shugabannin 'yan ta'addan ke ɓoye, musamman a cikin dajin tsohon wurin shakatawa na Oyo.
An kama mutane a wurare da dama a fadin ƙasar, wanda ya tilasta wa 'yan ta'addan sake dalibai da malaman ba tare da wani sharadi ba.
An bi hankali wajen tsara ayyukan don kaucewa cutarwa da kiyaye rayukan yaran da malamai. Duk da haka, jami'an tsaro sun samu wasu raunuka a yayin gudanar da aikin.

Kara karanta wannan
Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo

Source: Facebook
Ina daliban da aka ceton?
Punch ta wallafa cewa a yanzu haka, dalibai da malaman da aka tsare suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba kafin gwamnatin jihar Oyo ta karbe su.
Hafsan rundunar ya yi godiya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan jagorancinsa da tallafin da ya ba hukumomin tsaro.
Ya kuma gode wa Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da kuma dukkan mazauna jihar kan haɗin guiwarsu da hukumomin tsaro a lokacin aikin.
Jami'an soja sun bukaci al'ummar Najeriya da su ci gaba da ba hukumomin tsaro labarin da suka sani domin taimakawa wajen kare rayuka a fadin ƙasar nan.
An harbe 'yan bindiga
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya sun gwabza da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Ogun.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun 'yan sanda sun kutsa cikin dajin da 'yan ta'addan suka buya domin cafke su, inda daga nan aka fara fafatawa.
Bayan musayar wuta, jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kashe 'yan bindiga biyu tare da raunata da dama daga cikinsu kafin su tsere cikin daji.
Asali: Legit.ng
