Femi Adesina: Wasu Ministocin sun kai ga gabatar da rahoton aikin da su ka yi

Femi Adesina: Wasu Ministocin sun kai ga gabatar da rahoton aikin da su ka yi

- Zanga-zangar lumunar da aka fara a wasu jihohin ta canza salo, ta koma rikici

- Don haka Muhammadu Buhari ya bukaci Ministoci su je su zauna da Talakawa

- A makon jiya Shugaban kasa ya ba Ministoci umarni su je gida su duba lamarin

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Ministocinsa su kawo masa rahoton aikin da ya tura su.

Shugaban kasa ya ba duka Ministocinsa umarni su tafi garuruwansu, su lura da abin da ya auku wajen zanga-zangar #EndSARS, su kawo masa bayanai.

Muhammadu Buhari ya bada wannan umarni ne a wajen taron FEC da ake yi da ministoci da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya kowane mako.

KU KARANTA: Tsagerun da su ka yi sata a lokacin zanga-zanga za su tafi kukurku

Femi Adesina: Wasu Ministocin sun kai ga gabatar da rahoton aikin da su ka yi
Shugaba Buhari ya na jawabi Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya nemi ministocin gwamnatinsa su koma garuruwansu, su sa baki a kan zanga-zangar #EndSARS ta lumana, da ta rikide ta koma rikici.

Mai magana da yawun bakin Shugaban kasa, Femi Adesina ya tabbatar da cewa Buhari ya bada wannan aiki, kuma ya fara karbar raohoto daga ministoci.

Femi Adesina ya ce zuwa ranar Laraba, ministoci biyu ne kadai su ka bada rahotonsu, domin kuwa har cikin makon nan wasu ba su iya baro gida ba.

Ya ce: “Zan iya fada maku saboda an yi zaman FEC a jiya (ranar Laraba), shugaban kasa ya bukaci rahoto daga ministocinsa da su ka tafi aikin da aka tura su.”

KU KARANTA: Gwamnati za ta bi gida-gida domin gano kayan tallafin da aka sace a Adamawa

“Biyu daga cikinsu ne kurum su ka iya gabatar da rahotonsu a jiya (Larabar), saboda wasunsu su na jihohinsu, su na cigaba da aikin da aka sa su.” Inji Hadimin.

Ministocin Kudu maso gabas ba su iya shiga kauyukansu ba kamar yadda aka bukata saboda gwamnoni sun sa dokar hana fita a dalilin rikicin da ake ta yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel