APM Ta Ɗauko Batun Yadda Bola Tinubu Ya Kashe Kudin Tallafin Mai da Ya Cire a Najeriya

APM Ta Ɗauko Batun Yadda Bola Tinubu Ya Kashe Kudin Tallafin Mai da Ya Cire a Najeriya

  • Jam'iyyar adawa ta APM ta bukaci gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi cikakken bayanin kudaden da aka samu bayan cire tallafin mai
  • APM ta yi zargin cewa an tara fiye da Naira tiriliyan 20 daga lokacin da aka cire tallafin zuwa yanzu amma yan Najeriya ba su ga komai ba
  • Ta zargi gwamnatin jam'iyyar APC da gaza amfani da kudaden wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APM ta bukaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta fitar da cikakken bayani kan yadda aka yi da kudin tallafin mai da aka cire a Najeriya.

APM ta bukaci gwamnatin ta fito ta yi wa yan Najeriya bayanai mai inganci da za a iya gamsuwa da shi kan yadda aka kashe tiriliyoyin Naira da aka samu bayan cire tallafin fetur tun daga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar wa 'yan Najeriya hankali, ya yi alkawarin romon dimukradiyya

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ruwaito cewa jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Abubakar Yusuf, ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata.

APM ta yi zargin an tara N20trn

APM ta ce ta dauko wannan batu ne sakamakon matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa, tabarbarewar ababen more rayuwa da kuma gibin manyan ayyukan ci gaba da ake fuskanta a kasar nan.

Ta ce duk da cewa gwamnati ta samu sama da Naira tiriliyan 20 bayan cire tallafin mai, amma har yanzun ana fama da matsalolin rayuwa a Najeriya.

Jam’iyyar ta tunatar da cewa bayan Tinubu ya sanar a ranar 29 ga Mayu, 2023 cewa an cire tallafin mai, farashin litar fetur ya tashi daga kasa da N200 zuwa sama da N1,500.

A cewarta, hakan ya haifar da karin kudin sufuri, kayan abinci, kudin makaranta, kula da lafiya, hayar gidaje, wutar lantarki da sauran bukatun yau da kullum.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kausasa murya kan 'yan bindiga, ya ce a hada kai a yake su

An zargi gwamnatin Tinubu da gazawa

APM ta ce akwai rahotannin da ke nuna cewa an karkatar da yawancin kudaden da aka samu daga cire tallafin mai, yayin da jami'an gwamnati ke ci gaba da bayyana alkaluma da nasarorin da jam’iyyar ta kira marasa tushe.

Jam’iyyar ta ce:

“A karkashin gwamnatin APC, yunwa ta zama babbar matsala ta kasa. Iyalai da dama ba sa samun abin da za su ci a kullum.
"Kananan ‘yan kasuwa na rufe sana'o'insu saboda tsadar gudanar da harkokinsu, yayin da talauci da rashin aikin yi ke kara karuwa.”

Bukatar APM ga gwamnatin Tinubu

Ta ce ikirarin gwamnati cewa ana zuba kudaden cikin muhimman bangarori ba tare da gabatar da cikakkun alkaluma da ayyukan da aka aiwatar ba, ba abin karba ba ne.

A karshe, APM ta bukaci gwamnatin Tinubu ta wallafa cikakken rahoto da zai bayyana jimillar kudaden da aka samu daga cire tallafin mai, yadda aka kashe su, wadanda suka amfana da kuma sakamakon da aka samu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Fetur.
Yadda ake zuba wa mota fetur a daya daga cikin gidan mai a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tinubu zai dawo da tallafin mai?

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi magana kan kiran da 'yan kasa da masana ke yi na neman dawo da tallafin mai bayan tashin farashin litar fetur.

Gwamnatin ta jaddada cewa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, duk da karin farashin mai a kasuwannin duniya.

Ta ce sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara tun a 2023, ciki har da cire tallafin mai sun kasance muhimman matakai da suka samu goyon bayan cibiyoyin kudi na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262