NYIF: Fiye da mutum miliyan sun nemi tallafin sana'o'i na matasa a cikin sati uku - Buhari

NYIF: Fiye da mutum miliyan sun nemi tallafin sana'o'i na matasa a cikin sati uku - Buhari

- Shugaban Buhari ya ce sama da mutum miliyan ɗaya ne suka cike tallafin NYIF tun bayan bude shafin cike tallafin a yanar gizo ranar 12 ga watan Oktoba, 2020.

- Buhari ya ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da gwamnatinsa ta ƙirƙiri dama irin wannan ga matasa ba

- A cewar Buhari, gwamnatinsa ta ƙirƙiri tsare-tsare sama da 25 don cigaban matasa

Shugaban ƙasa Muhammad Buhari yace sama da mutane miliyan ɗaya ne suka cike tallafin sana'o'i na matasa(NYIF)cikin sati uku da buɗe cike tallafin tun 12 ga watan Oktoba,2020.

Buhari,wanda ministan tarayyar Muhammad Bello ya wakilta,ya bayyana saƙon a ranar murnar matasa a ranar Lahadi.

Tallafin NYIF, wanda ya samu sahalewa daga hukumomin tarayya (FEC) a ranar 22 ga watan Yuli, 2020, an yi shine don tallafawa mutane masu karanchin shekaru; daga shekara 18 zuwa 35, kuma zai kai tsawon shekaru uku (2020-2023).

"Wannan kuɗaɗe an waresu musamman don zuba jari a tunani, fikira da fasahar matasan Najeriya domin basu damar kasuwanci, da abubuwan da ake buƙata don ƙirƙirar sana'o'i.

"Sama da mutane miliyan ɗaya suka samu damar cike tallafin tun bayan buɗe shafin yanar gizo na tallafin NYIF a ranar 12 ga watan Oktoba 2020", a cewarsa.

KARANTA: Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen man fetur

Buhari ya bayyana matasa a matsayin masu kawo sauyi a ƙasa a ɓangarorin zamantakewa, ɓunkasa tattalin arziƙi, da kuma samun cigaba mai ɗorewa.

NYIF: Fiye da mutum miliyan sun nemi tallafin sana'o'i na matasa a cikin sati uku - Buhari
Buhari da shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya
Asali: UGC

Buhari yace gwamnatinsa ta ƙirƙiri tsare-tsare sama da 25 musamman don inganta rayuwar matasa a faɗin ƙasa.

A cewar Buhari, tsare-tsaren gwamnatinsa don matasa sun haɗar da:

Tsarin cigaban matasan Najeriya (NYP), Nigeria Youth investment fund(NYIF) wanda aka kaddamar a watan Juli 2020,Tsarin DEEL,wanda aka warewa Naira biliyan huɗu ₦4b don gudanarwa.

KARANTA: Yadda za a duba sakamakon jarrabawar WAEC cikin sauki ta hanyar bin matakai 7

Sauran sun haɗar da sahalewar dokar bawa matasa damar mulki (#Not too young to run.), N-power, Tsarin P-YES, Tsarin YES, tsarin YouWIN, tsarin GIS da sauran su.

Buhari ya ƙara da ''cewa matasa sune ƙashin bayan al-umma wanda zasu kai ƙasa ga ci. Idan matasa suka zamo tsintsiya babu irin ƙalubalen da ƙasa zata fuskanta basu tunkareshi ba .

"A wannan rana ta musamman, munyi amanna da yaƙinin cewa wannan mahaluƙiyar kasa wadda ake kira Najeriya da makomarta rankatakaf na hannunku; matasa.

''Mun fuskanci ƙalubale da dama, amma wanzuwarku ta baiwa ƙasa kwarin guiwar tunkarar dukkan wani ƙalubale da take fuskanta."

A wani labarin daban da Legit.ng Hausa ta wallafa, shugaba Buhari ya yi alhini tare da mika sakon ta'aziyyar rasuwar babban limamin cibiyar Musulunci ta Uthman Bin Affan da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng