Yadda taron Buhari da tsofaffin Shugabannin Najeriya a Aso Villa ya kasance
- Femi Adesina ya bada labarin ganawar tsofaffin shugabanni da Shugaban kasa
- Hadimin shugaban kasar ya ce tsofaffin shugabannin sun ba Buhari shawarwari
- Wadanda su ka halarci taron sun hada da Dr. Jonathan, Babangida, da Obasanjo
Mai taimaka wa shugaban Najeriya wajen yada labarai, Mista Femi Adesina ya yi magana game da taron da mai gidansa ya yi da tsofaffi shugabanni.
A ranar 23 ga watan Oktoba, 2020, Muhammadu Buhari ya gana da sauran wadanda su ka taba rike mulkin Najeriya, Adesina ya ce an motsi a zaman.
Jaridar Punch ta rahoto Hadimin shugaban kasar ya na cewa an tattauna lamarin #EndSARS da kuma sauran batutuwan da su ka shafi halin kasa a taron.
KU KARANTA: Ja’irai sun fake da #EndSARS, sun gutsere al’aurar 'Dan Sanda
Wadanda su ka samu halartar wannan zama su ne: Olusegun Obasanjo, Ibrahim Badamasi Babangida, Ernest Shonekan, da Abdulsalami Abubakar.
Yakubu Gowon da tsohon shugaba Goodluck Jonathan wanda ya mika wa Buhari mulki ya hallara.
Janar Yakubu Gowon ya ba gwamnatin Muhammadu Buhari shawarin da za su taimaka a matsayinsa na wanda ya yi jagoranci lokacin yakin basasa.
Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana tare da tsoron za ayi tunanin ya na sukar gwamnati mai-ci. Obasanjo yay aba wa shugaban kasa game da jawabin da ya yi.
KU KARANTA: Gwamnoni sun soki tsarin albashin da Buhari ya kirkiro wa Malamai
Da aka zo kan Ibrahim Babangida, shi kuma ya nuna damu wa game da aikin jami’an tsaro, ya koka a kan irin bayanan da hukuma ta ke samu a harkar tsaro.
Abdussalami Abubakar ya ce akwai bukatar a samu hadin-kai sosai tsakanin duka jami’an tsaro, ya kuma yi gargadi a kan kutse da ake samu wajen aiki da juna.
A na sa bangaren, Ernest Shonekan ya yi kira a dauki matakan rigakafi tun wuri. Shi ma Goodluck Jonathan ya yi magana, ya yabi jawabin shugaban kasar.
A baya kun ji cewa shugaban kasa ya bukaci fara ganin sakamakon aikin da ya tura Ministoci su yi a gida bayan zanga-zangar EndSARS ta rikida, ta zama rigima.
Ministoci 2 cikin 43 ne su ka mika wa Buhari rahoto game da rikicin #EndSARS a jihohinsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng