Tinubu/Shettima: Matsayar Kiristocin Arewa kan Daukar Kashim a Mataimaki
- Wata kungiyar Kiristoci a yankin Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki
- Shugaban kungiyar, Fasto Jolly Usman, ya ce ƙwarewar Shettima da haɗin gwiwarsa da Tinubu sun taimaka wajen inganta tsaro
- Ƙungiyar ta bukaci 'yan Najeriya su yi hukunci kan shugabanni bisa ayyukansu da nagartarsu, ba wai la'akari da bambancin addini kaɗai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Ƙungiyar Middle Belt Pentecostal Association (MPA) ta bayyana goyon bayanta ga zabin mataimaki da Bola Tinubu ya yi.
Kungiyar ta yabawa matakin Bola Tinubu na ci gaba da riƙe Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, ƙungiyar ta ce wannan mataki alama ce ta dorewar shugabanci, tabbatar da kwanciyar hankali da kuma jajircewa wajen ci gaban Najeriya, cewar The Guardian.
Dalilin kungiyar na mara wa matakin Tinubu baya
Shugaban MPA, Fasto Jolly Usman na Grace Assembly, ya bayyana cewa tikitin Tinubu da Shettima na nuna shugabanci mai hangen nesa wanda ke mayar da hankali kan magance matsalolin da ke addabar Arewa da yankin Middle Belt.
Wannan matsaya ta zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan daidaiton addini a tikitin shugaban ƙasa, inda ƙungiyar ta jaddada cewa ya kamata a fi duba nagartar shugabanci da ayyukan gwamnati maimakon bambancin addini.
Fasto Usman ya ce suna maraba da shawarar Shugaba Tinubu ta ci gaba da zaɓar Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa ci gaban da ake samu ƙarƙashin manufar Renewed Hope Agenda.
Ya ƙara da cewa Kiristocin Arewa sun ga ci gaba a fannin ababen more rayuwa, matakan inganta tsaro a Middle Belt da kuma ƙoƙarin rage gibin ci gaba tsakanin al'ummomi.

Source: Twitter
Kashim Shettima ya sha ruwan yabo
Ƙungiyar ta kuma yabawa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima kan rawar da yake takawa wajen ƙarfafa haɗin kan mabiya addinai daban-daban da kuma tallafa wa ayyukan jin ƙai a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

Kara karanta wannan
Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027
Ta buƙaci 'yan Najeriya su tantance tikitin shugaban ƙasa bisa ingancin shugabanci da sakamakon ayyukan gwamnati, ba wai la'akari da tsarin addinin 'yan takara kawai ba, cewar Vanguard.
A cewar Fasto Usman, haɗin gwiwar Tinubu da Shettima ya samar da sakamako mai kyau a fannoni kamar noma, ilimi da samar da zaman lafiya, waɗanda suka amfani al'ummomin yankin.
Ya ce kafin ƙungiyar ta bayyana matsayarta, ta tattauna da majami'un da ke ƙarƙashinta, inda mafi yawan mambobinsu suka amince cewa shugabancin da ake da shi yanzu shi ne mafi dacewa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba.
Zaben 2027: Shettima ya ziyarci Tinubu
Mun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sa labule da shugaba Bola Ahmed Tinubu jim kadan bayan an tabbatar masa kujerarsa a takarar 2027.
A ranar Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2026 ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen rade-radin wanda zai zama abokin takararsa a zabe mai zuwa.
An jima ana rade-radin cewa bai dace Tinubu ya tafi da Shettima ba domin a ba wa kirista dama ya zama mataimakin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng
